Shugaban Majalisar Dattawa Ya Jero Jihohin da APC Ke Shirin Kwacewa Daga Hannun 'Yan Adawa
- Sanata Godswill Akpabio ya yi ikirarin cewa APC mai mulki zata karɓi jihohin Kudu maso Kudu a zabe na gaba
- Shugaban majalisar dattawan ya ce ya kamata shiyyar ta gode wa Shugaban Ƙasa Tinubu ta hanyar zaɓen jam'iyyar APC
- Ya ce duk da yadda ake kallon Kudu maso Kudu, Tinubu ya samu kaso 25 cikin 100 da ake buƙata a jihohin yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya ce jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ga wurin zama a shiyyar Kudu maso Kudu.
Ya ce hanya ɗaya da shiyyar zata godewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na baiwa ɗansu kujera lamba ta uku a Najeriya, shi ne APC ta samu nasara a yankin.
A cewar Akpabio, a karo na farko cikin shekaru 45, Tinubu ya ba Kudu maso Kudu kujerar shugaban majalisar dattawa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Akpabio ya yi wannan furucin ne yayin da ya karɓi bakuncin mambobin majalisar zartarwa na APC reshen yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.
Wane jihohi APC ke shirin karɓewa?
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce Bola Tinubu da jagororin APC sun yi wa yankin gata, ta hanyar miƙa musu kujera mai daraja ta uku a tsarin mulkin ƙasar nan.
Sakamakon haka ya ce ya zama dole su maida biki bisa wannan karamci ta hanyar buɗa wa APC hanyar lashe zaben dukkan jihohin Kudu maso Kudu a zaɓe na gaba.
Da yake tsokaci kan zaben 2023, Sanata Akpabio ya jaddada cewa shugaba Tinubu da APC sun samu kaso 25% na kuri'un da doka ta tanada a dukkan jihohin Kudu maso Kudu.
Ya ƙara da cewa a jihar Akwa Ibom kaɗai, "APC ta samu kuri’u fiye da yadda ta samu a jihohin Kudu maso Gabas guda biyar idan aka haɗa su wuri ɗaya."
Don haka ya bukaci shugabannin APC na shiyyar da su yi aiki tukuru don ganin APC ta lashe zaben gwamna na shekara mai zuwa a jihar Edo, cewar rahoton Premium Times.
Kwankwaso ya faɗa rami a NNPP
A wani rahoton kuma Shugabannin NNPP na shiyyar Arewa maso Gabas sun juyawa Rabiu Kwankwaso baya, sun ce suna goyon bayan korar da aka masa.
Mambobin majalisar zartarwa da masu ruwa da tsaki na NNPP a shiyyar sun zargi Kwankwaso da hannu a rikocin cikin gida da ke faruwa.
Asali: Legit.ng