Wike vs Fubara: Jerin Sunayen Manyan Yan Siyasa 4 da Tsohon Gwamnan Ribas Ya Raba Gari da Su

Wike vs Fubara: Jerin Sunayen Manyan Yan Siyasa 4 da Tsohon Gwamnan Ribas Ya Raba Gari da Su

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Port Harcourt, Jihar Rivers - Jihar Ribas na fama da rikicin siyasa tun a karshen watan Oktoba lokacin da wasu yan majalisa suka yi kokarin tsige Gwamna Siminalayi Fubara.

Ana ganin yan majalisar da suka yi yunkurin tsige gwamnan sun yi hakan ne bisa umurnin Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya.

Wike ya raba gari da wasu manyan yan siyasa hudu
Wike vs Fubara: Jerin Sunayen Manyan Yan Siyasa 4 da Tsohon Gwamnan Ribas Ya Raba Gari da Su Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Egele Micah, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Majalisar jihar ta rabu gida biyu tun a watan Oktoba - Martin Amaewhule shine kakakin yan majalisa da dama wadanda ke tare da Wike yayin da Edison Ehie shine kakakin majalisar masu biyayya ga Gwamna Fubara.

Legit Hausa ta rahoto cewa watanni bakwai da suka gabata, akwai alaka mai kyau tsakanin Wike da Fubara. Amma ba Fubara bane mutum na farko da Wike ke raba gari da shi. Ga sauran a kasa:

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya maida zazzafan martani yayin da ake shirin tsige shi daga kan mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1) Rotimi Amaechi

Wike ya yi aiki a matsayin shugaban ma'aikatan Rotimi Amaechi lokacin da yake matsayin gwamnan Ribas.

A 2011, Wike ya koma Abuja a matsayin karamin ministan ilimi.

Sai dai kuma, tun 2014 lokacin da Amaechi ya bar PDP zuwa APC a karshen wa'adin mulkinsa na biyu a matsayin gwamna, yan siyasar biyu sun kasance a jam'iyyu daban-daban sannan suka zama abokan hamayya.

Yayin da Wike ke ci gaba da kasancewa a PDP, Amaechi da wasu gwamnoni sun sauya sheka zuwa APC da aka kafa.

2) Atiku Abubakar

Rikici ya fara tsakanin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2019 da 2023, da Wike a 2022.

Wike ya raba gari da shugabancin PDP tun bayan da ya sha kaye a hannun Atiku a zaben fidda gwani a watan Yunin 2022. Koda dai ya sha nanata cewa shi dan PDP ne har yanzu, ana ganin Wike ya tarawa babban abokin hamayyar Atiku, Bola Tinubu na APC kuri'u a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da ke tsaka mai wuya ya samu natsuwa bayan 'yan majalisun Tarayya sun yi masa abu 1 tak

Domin nuna godiya ga gudunmawar da Wike ya ba shi a zaben shugaban kasa na 2023, Tinubu ya nada shi ministan Abuja.

A watan Satumba, shugaban kasar ya yaba masa (Wike) kuma ya ce Wike ba ministan Abuja bane kawai illa mai ba shi shawara.

3) Chidi Lloyd

A karshen 2022, tsohon dan majalisar dokokin jihar Ribas, Chidi Lloyd, ya ba Wike hakuri kan caccakar gwamnatinsa. Kafin wannan al'amari inda Lloyd ya fashe da kuka a bainar jama'a, yan siyasar biyu suna da kyakkyawar alaka.

Lloyd, wanda aka gano cikin hawaye a wani bidiyo da ya yadu, ya bayar da hakurin ne yayin da yake jawabi wajen kaddamar da aikin hanyar Akpabu-Omudioga-Egbeda a Nuwamban 2022.

Lloyd shine shugaban karamar hukumar Emohua mai ci a yanzu.

Kalli bidiyon a kasa:

4) Sim Fubara

Makusantan biyu - Wike da Fubara - suna nan dumu-dumi a rikicin siyasar da ke gudana yanzu haka a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Muhimman dalilai 3 da ka iya sa a tsige gwamnan PDP daga kan mulki

Bayan wata ganawa da wasu gwamnonin PDP a Abuja, Wike ya zargi Fubara da hulda da abokan hamayyarsa a siyasa. Ministan ya kuma zargi Fubara da bata tsarin siyasar da shi (Wike) ya kafa.

Musabbabin rikicin Wike da Fubara

A wani labarin, mun ji cewa an bayyana musabbabin abin da ya haddasa rikici a tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da Nyesom Wike.

Jaridar The Punch ta tattaro cewa Wike ne ya miƙa jerin sunayen kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da sauran manyan muƙamai da muƙamansu ga Gwamna Siminalayi Fubara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel