Gaskiya Ta Ƙara Bayyana Kan Ruɗanin da Aka Gani a Kwafin Hukuncin Tsige Gwamna Abba Na Kano

Gaskiya Ta Ƙara Bayyana Kan Ruɗanin da Aka Gani a Kwafin Hukuncin Tsige Gwamna Abba Na Kano

  • Felix Morka ya ce kuskuren ɗan adam aka samu a kwafin hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige gwamnan Kano
  • Kwafin hukuncin CTC ya nuna ƙarara a karshe cewa Abba Kabir Yusuf ne gwamnan Kano, lamarin da ya ja hankalin yan Najeriya
  • Sai dai kakakin APC na ƙasa ya ce ba a ɗaukar matsaya daga karanta wani bangare na shari'a musamman a kotun ɗaukaka ƙara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sakataren watsa labaran APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce ruɗanin da aka samu a kwafin takardar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara (CTC) na zaben gwamnan Kano kuskure ne na ɗan adam.

Sakataren watsa labaran APC ta ƙasa, Felix Morka.
Kano: Takardun hukuncin Kotun daukaka kara kuskure ne na dan adam, Morka Hoto: Felix Morka
Asali: UGC

Morka ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels cikin shirin siyasa a yau.

Kara karanta wannan

Sabon tashin hankali ya ɓullo yayin da kotun koli ke shirin yanke hukunci kan nasarar gwamnan arewa

Idan baku ma ta ba kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun zaɓe na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma a karshe-ƙarshe daidai shafi na 67 da ke kunshe a cikin kwafin hukunci, an ga kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin kotun zaɓe, wanda ya sauke Abba daga kujerar gwamna.

Daily Trust ta tattaro cewa da yake jawabi a hirar, Mista Morka ya ce:

"Ba zai yuwu ka karanta hukuncin guntu-gunto ko ku keɓe wani sashi ku karanta ba, sha'anin shari'a musamman a kotun daukaka ƙara, ana yanke hukunci bisa hujjoji."
"Idan aka gabatar da batutuwa biyu ko uku a gaban kotu, kuma ta yanke hukunci kan na farko, na biyu da na uku duk ta baiwa wata jam'iyya nasara, ba zai yuwu ƙarshe ya saɓawa farko ba, matsalar da aka samu kenan a shari'ar Kano."

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Sakkwato

"Sun ce wanda ake ƙara kuma suka dawo suka ce wanda ya shigar da ƙara, wannan abu ne da ke faruwa lokaci bayan lokaci, shi kansa wanda ya rubuta hukuncin a na'ura zai iya yin kuskure saboda sauri."

Kakakin APC ya ce abinda ya fi muhimmanci shi ne kotun ɗaukaka ƙara ta fito ta yi bayanin kuskuren da aka samu kuma ta gyara.

Obaseki ya ce wuƙa da nama na hannun PDP

A wani rahoton na daban Obaseki ya ce mambobin PDP ne kaɗai za su yanke ko Shuaibu zai zama dan takarar gwamna a inuwar jam’iyyar a zaben Edo ko akasin haka.

Godwin Obaseki ya yi wannan furucin ne jim kaɗan bayan ganawa da Gwamna Bala Muhammaed na jihar Bauchi ranar Alhamis

Asali: Legit.ng

Online view pixel