Sabon Tashin Hankali Ya Ɓullo Yayin da Kotun Ƙoli ke Shirin Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan Arewa

Sabon Tashin Hankali Ya Ɓullo Yayin da Kotun Ƙoli ke Shirin Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan Arewa

  • Watanni da dama bayan kammala babban zaben 2023 a Najeriya, har yanzun kotuna na kokarin warware korafe-ƙorafen da suka biyo baya
  • Duk da a halin yanzu abun ya sha kan kotunan zaɓe, kotun ɗaukaka ƙara da kotun koli na ci gaba da yanke hukunci
  • A jihar Nasarawa, akwai takun saƙa tsakanin Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC da babbar jam'iyyar adawa watau PDP

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Yayin da ake dakon hukuncin kotun kolin Najeriya a karar zaben gwamnan jihar Nasarawa, fargaba da tashin hankali sun fara yawaita a jihar.

Manyan jam'iyyun siyasa biyu, PDP da APC, dukkansu sun shiga kotu suna ikirarin cewa ɗan takararsu ne ya lashe zaben watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta garzaya kotun koli don kalubalantar shari'ar gwamnan APC, ta koka da zaluncin kotu

Tashin hankali a Nasarawa gabanin hukuncin kotun koli.
Tashin Hankali a Jihar Nasarawa Yayin da Ake Dakon Hukuncin Kotun Koli Hoto: @Garshehu @Atiku
Asali: Twitter

Da farko, kotun sauraron kararrakin zabe ta tsige Gwamna Abdullahi Sule na APC kana ta ayyana ɗan takarar PDP, David Ombugadu a matsayin sahihin wanda ya ci zaɓen gwamna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma da batun ya kai gaban kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja, ta soke hukuncin kotun zaɓe kana ta tabbatar da nasarar Gwamna Sule.

Tashin hankali na ƙaruwa a Nasarawa

Ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba, 2023, jam'iyyar APC ta yi zargin cewa PDP na kulle-kulle shirya zanga-zangar tada hankali domin zafafa yanayin siyasa da tada zaune tsaye.

Kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro, APC ta bayyana cewa ta gano mummunan shirin PDP na tada yamutsi da sunan zanga-zanga.

Shugaban APC na jihar Nasarawa, Aliyu Bello, a wata hira da yan jarida ya ce tun da kotun ɗaukaka ƙara ta bai wa Abdullahi Sule nasara, jam'iyyar PDP ta ci gaba da kulla makirci.

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Sakkwato

A rahoton Vanguard, ya ce:

"Wannan jihar ta kowace, bai kamata a ji muna karfafa tare da goyon bayan munanan kalamai da ɗabi'u waɗanda ba su da matsuguni a tushen tarihin mu ba."

A nata ɓangaren, jam'iyyar PDP reshen jihar Nasarawa ta gudanar da zanga-zanga a Lafia, babban birnin jihar ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba.

Ta kuma roƙi kotun koli ta yi dogon nazari kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, "da nufin tabbatar da tsarin demokuraɗiyya a Najeriya."

Kakakin APC ya faɗi matsalar da aka samu a hukuncin Kano

A wani rahoton kuma Mai magana da yawun APC ta ƙasa, Felix Morka, ya bayyana asalin inda aka samu matsala a takardun hukuncin tsige Abba na Kano.

Kwafin hukuncin CTC ya nuna ƙarara a karshe cewa Abba Kabir Yusuf ne gwamnan Kano, lamarin da ya ja hankalin yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel