Shehu Sani Ya Bayyana Kotun da Ya Kamata Dino Melaye Ya Je Domin Kalubalantar Zaben Gwamnan Kogi

Shehu Sani Ya Bayyana Kotun da Ya Kamata Dino Melaye Ya Je Domin Kalubalantar Zaben Gwamnan Kogi

  • Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce yana goyon bayan matakin Sanata Dino Melaye na ƙin zuwa kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen gwamnan Kogi
  • Ɗan takarar na PDP ya zo na uku a bayan wanda ya lashe zaben, Usman Ododo na APC da Murtala Ajaka na SDP
  • Sani ya ce idan har Sanata Melaye ya yanke shawarar tunkarar kotu domin kalubalantar zaɓen, to lallai ya zama kotun “Tennis” ce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Lokoja, jihar Kogi - Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya mayar da martani ga ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a ƙarkashin jam'iyyar PDP, Sanata Dino Melaye, kan ƙin zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Babban malamin addini ya yi magana kan yiwuwar sasanta wa tsakanin Wike da Fubara

Shehu Sani ya shawarci Dino Melaye
Shehu Sani ya ba Dino Melaye shawara Hoto: Shehu Sani/Dino Melaye
Asali: Facebook

Sani ya ce yana goyon bayan matakin Melaye na ƙin zuwa kotu bayan ya zo na uku a bayan ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Usman Ahmed Ododo da Murtala Ajaka na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).

Ya bayyana cewa idan Melaye ya yanke hukuncin zuwa kotu, to tabbas ta kasance kotun ta Tennis ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne ta shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @ShehuSani, a ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

"Ina goyon bayan Dino kada ya je kotu, idan ya zama dole, to kawai ya je ta wasan Tennis."

Dino Melaye ya sha alwashin ƙin zuwa kotu

Sanata Dino Melaye na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ɗan takarar gwamna a jihar Kogi, ya ce ba zai tafi kotun zaɓe domin ƙalubalantar nasarar da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu ba.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan nasarar Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna

Melaye ya jadada cewa a halin yanzu bangaren shari'a ba ta adalci, kuma ta zama wani sashi ne na APC.

Fani-Kayode Ya Caccaki Dino Melaye

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Femi Fani-Kayode ya yi wa Dino Melaye ba'a kan kayen da ya sha a zaɓen gwamnan Kogi.

FKK ya bayyana kayen da Dino ya sha a zaben gwamnan na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, a matsayin gagarumin koma baya a harkar siyasarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng