Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Zaben Dan Majalisar PDP, Ta Yi Hukuncin Bazata
- Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta karisa hukuncin shari'ar zaben Majalisar jihar Plateau a ranar Laraba
- Kotun ta rusa zaben dan takarar jam'iyyar PDP, Cornelius Doeyok da ke wakiltar mazabar Quaanpan da ke jihar
- Har ila yau, kotun ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar APC, Farfesa Theodore Bala Maiyaki a matsayin wanda ya lashe zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Kotun daukaka kara ta raba gardama kan shari'ar zaben Majalisar jihar Plateau.
Kotun da ke zamanta a Abuja ta kwace kujerar Cornelius Doeyok na jami'yyar PDP mai wakiltar mazabar Quaanpan ta Kudu.
Wane hukunci kotun ta yanke?
Kotun ta kwace kujerar ce kan dalilin cewa PDP ba ta da tsari da za ta dauki nauyin 'yan takararta a zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Doeyok shi ne mamban jami'yyar PDP da ya rage a kujerar inda dukkan kujerun APC ta kwace a kotu, cewar Daily Trust.
Yayin hukuncin kotun, Mai Shari'a, Abdu-azeez Wazi ya tabbatar da nasarar Farfesa Theodore Bala Maiyaki na APC a matsayin wanda ya lashe zaben.
Wane umarni kotun ta bai wa hukumar zabe?
Har ila yau, kotun ta umarci hukumar zabe ta INEC ta kwace satifiket na cin zabe daga hannun Doeyok ta bai wa Maiyaki.
Bayan wannan hukunci, a yanzu haka jami'yyar PDP mai mulki a jihar ta rasa dukkan kujerunta guda 16, cewar TheCable.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kwashe kusan dukkan kujerun har guda 22 yayin da jami'yyun YPP da LP ke da kujera dai-dai.
Kotu ta yi hukunci a zaben Majalisa a Gombe
A wani labarin, kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci ka shari'ar zaben kakakin Majalisar jihar Gombe.
Kotun ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar APC kuma kakakin Majalisar jihar, Abubakar Luggerewo.
Har ila yau, kotun ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Bashir Gaddafi kan rashin hujjoji a zaben da aka gudanar a mazabar Akko ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng