Batun Shari’ar Zaben Kano Ya Yi Girma, NNPP Ta Kai Magana Zuwa ECOWAS, EU da Amurka

Batun Shari’ar Zaben Kano Ya Yi Girma, NNPP Ta Kai Magana Zuwa ECOWAS, EU da Amurka

  • NNPP tayi zanga-zanga a ofishin jakadancin kasashen Birtaniya da Amurka saboda hukuncin shari’ar gwamnan jihar Kano
  • Jam’iyyar ta ce akwai yunkurin da ake yi na zaluntar al’ummar Kano, a karbe mulki daga hannun Abba Kabir Yusuf da aka zaba
  • Shugabannin NNPP sun je har ofishin ECOWAS, su ka bukaci ayi adalci a shari’ar zaben Kano ko kuwa rikici ya barke a Afrika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ta kai zanga-zangarta zuwa Abuja saboda abin da ta kira neman soke nasararta a zaben 2023.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa shugabannin NNPP sun ce idan har aka karbe gwamnatin Kano daga hannunsu, za a iya haddasa rikici.

NNPP.
Zanga-zangar NNPP a Abuja Hoto: Kwankwaso Twitter @babarh
Asali: Twitter

Ladipo Johnson ya jagoranci 'Yan NNPP

Kara karanta wannan

Alkalan da suka yi kuskure a shari’ar zaben Kano za su yabawa aya zaki a Majalisar Shari’a

A wani jawabi da Ladipo Johnson ya fitar a ranar Laraba, ya yi gargadi cewa wannan rigima za ta iya shafan har sauran kasashe na Afrika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban mai binciken kudi ya karanto jawabin da shugaban jam’iyyar NNPP na rikon kwarya, Abba Kawu Ali ya rubuta a ofishin ECOWAS.

NNPP ta kuma yi tattaki zuwa ofishin jakadancin Amurka da na Birtaniyya da babban ofishin kungiyar EU ta tarayyar Turai a garin Abuja.

"Ana so a zalunci mutanen Kano" - NNPP

Shugabannin na NNPP sun ce daga hukuncin kotun sauraron karar zabe da na daukaka kara, ta fito cewa ana so a zalunci mutanen Kano.

Jawabin Abba Kawu Ali ya ce mafi yawan al’umma sun zabi Abba Kabir Yusuf da NNPP a watan Maris, amma ana shirye-shirye domin a tsige shi.

Jawabin ya ce a yanzu abubuwa sun canza a Kano domin kuwa jama’a su na jin an cuce su.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Sai da NNPP ta tafka magudi sannan ta samu nasara a Kano, Ado Doguwa

Jam’iyyar ta ce ba za ta yi wasa da batun takardun hukuncin CTC da aka fitar ba, Vanguard take cewa NNPP za ta shelantawa duniya.

Jam'iyyar NNPP ta yi babban kira

"Mu na so ku yi wa gwamnatin Najeriya, shugaban kasa da shugaban shari’a magana cewa dole ayi wa Kano hukunci da dokar kasa.
Shakka babu, maganar ta na kotun koli, amma Kanawa su na jin an zalunce su a kotun daukaka kara inda aka samu sabani a CTC."

- Ladipo Johnson

Kiran da jam’iyyar ta yi ya hada da Kashim Shettima, gwamnoni, sanatoci, da kuma malamai.

Sanata ya ce ana so a dawo da APC mulkin Kano

Ana da labari Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi Allah wadai da hukuncin shari’ar Gwamna Abba Kabir Yusuf da APC da aka yi a kotu.

Sanatan na Kano ya ce ana shirin tsige Abba Kabir Yusuf, a mika mulki ga wanda ya san bai lashe zabe ba, har ya taya NNPP murna a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng