Tinubu Ya Aike da Sako Ga Majalisar Dattawa, Ya Nemi Ta Amince da Naɗin Shugaban ICPC

Tinubu Ya Aike da Sako Ga Majalisar Dattawa, Ya Nemi Ta Amince da Naɗin Shugaban ICPC

  • Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wasiƙar neman hanzarta amincewa da naɗin sabon shugaban ICPC zuwa ga majalisar dattawa
  • A takardar da shugaban ƙasan ya aika, ya nemi ta amince da naɗin wasu ƙarin mutum biyu a matsayin mambobin hukumar shari'a ta tarayya
  • A makon da ya wuce ne, shugaban kasa ya naɗa Dokta Adamu Aliyu a matsayin sabon shugaban hukumar yaƙi da rashawa (ICPC)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rubuta wasiƙa, ya aike ga majalisar dattawa kan naɗin sabon shugaban hukumar yaƙi da rashawa (ICPC).

Tinubu ya roƙi majalisar ta duba yuwuwar gaggauta amince wa da naɗin Adamu Aliyu a matsayin shugaban hukumar ICPC na ƙasa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya aike da saƙo ga majalisar dattawa.
Tinubu Ya Aike da Sako Ga Majalisar Dattawa, Ya Nemi Ta Amince da Naɗin Shugaban ICPC Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Haka nan kuma naɗin Saka Bolaji Suleiman da Farfesa Dantata a matsayin mambobin gudanarwa na hukumar kula da harkokin shari'a ta ƙasa na cikin takardar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Peter Obi Ya Magantu Bayan Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Karar da Ya Daukaka

Waɗan nan naɗe-naɗe biyu na ƙunshe a takardar da Tinubu ya aika zuwa ga shugaban majalisar dattawa, inda ya nemi a hanzarta amince wa da su gaba ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon jiya Tinubu ya naɗa Aliyu

Sama da mako ɗaya da ya shige, Bola Tinubu ya naɗa Dokta Aliyu a matsayin shugaban hukumar ICPC, a wata sanarwa da Ajuri Ngelale, kakakin shugaban ƙasa ya fitar.

A rahoton Premium Times, Sanarwan ta ce:

"An naɗa sabon shugaban ICPC ne gabanin majalisar dattawa ta tantance kuma ta tabbatar da shi bayan amincewar shugaban ƙasa."
"Wannan ya biyo bayan amincewar shugaba Tinubu da buƙatar tsohon shugaban ICPC wanda ya nemi tafiya hutun karewar wa'adinsa daga ranar 4 ga watan Nuwamba, 2023 kafin ya sauka ranar 3 ga Fabrairu, 2024."

A cewar Ajuri, an yi nadin ne “domin ci gaba da sabunta fatan yan ƙasa da sake fasalin manyan cibiyoyi da kuma karfafa yakin da Najeriya ke yi da cin hanci da rashawa.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ƙara Yin Gyara, Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar ECN Ta Ƙasa

Jerin kasashen da babu jakadun Amurka

A wani labarin kuma Amurka ta koka kan rashin jakadu a kasashen duniya akalla 31 ciki har da Najeriya da kuma Masar watau Egypt.

Mun tattaro muku jerin sunayen dukkan waɗan nan ƙasashe baya ga Najeriya kuma babban dalilin da ya sa har yanzu ba su da jakadun Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel