Alkalan Da Suka Yi Kuskure a Shari’ar Zaben Kano Za Su Yabawa Aya Zaki a Majalisar Shari’a

Alkalan Da Suka Yi Kuskure a Shari’ar Zaben Kano Za Su Yabawa Aya Zaki a Majalisar Shari’a

  • NJC ba za ta bari kuskuren da aka tafka wajen shari’ar zaben sabon gwamnan Kano na 2023 ya tafi haka a banza ba
  • Majalisar shari’ar za ta hukunta Alkalan da ake zargi da hannu wajen abin kunyan da aka samu a takardun CTC
  • Moore Aseimo Abraham Adumein ya yanke hukunci a shari’ar da Abba Kabir Yusuf ya daukaka, ya ba APC nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Majalisar NJC da ke kula da Alkalai ta shira yin bincike game da abin maganar da aka jawo a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano.

Daily Trust ta ce kura-kuren da aka samu a takardun hukuncin CTC na shari’ar zaben gwamnan Kano ya jawo majalisar NJC za tayi bincike.

Kara karanta wannan

Kawu Sumaila: Sanatan NNPP Ya fede gaskiya a shari’ar zaben Gwamnan Jihar Kano

Gwamnan Kano
Gwamnan jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Za a hukunta Alkalan shari'ar Kano

Jami’an NJC wanda su ke da alhakin korar Alkali idan ya yi laifi sun tabbatar da haka lokacin da su ka ziyarci manema labarai a garin Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani jami’in majalisar ya shaidawa cewa sun samu korafe-korafe a kana bin da ya faru a shari’ar Kano, kuma za a dauki matakin da ya dace.

A cewarsa, za a shirya cikakken bincike ta hanyar kafa kwamiti na musamman, sannan a zartar da hukunci kamar yadda dokar NJC ta tanada.

Wani mataki Abba Kabir Yusuf ya dauka?

Babban jami’in yake cewa duk da lauyan Abba Kabir Yusuf ya ce za su kai maganar zuwa kotun koli, wannan ba zai hana NJC yin bincikenta ba.

Wole Olanipekun ya ki dawo da takardun CTC da kotun daukaka kara ta bada, ya ce lokacin da za a iya yin wani gyara tuni ya wucewa alkalan.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban INEC, Jega Ya Soki Hukuncin Zaben Kano, Ya ba Tinubu Shawara

Jaridar Leadership a wani rahoto da ta fitar a tsakiyar makon nan ta ce majalisar ta NJC ta fara kokarin yin gyara a sanadiyyar surutun jama’a.

Su wanene Alkalan shari'ar Kano?

Mai shari’a Moore Aseimo Abraham Adumein ne shugaban zama a shari’ar da Abba Kabir Yusuf ya dauka zuwa kotun da ke zama a garin Abuja.

Baya ga da ke kotun daukaka kara da ke garin Ibadan, Bitrus Gyarazama Sanga da Lateef Adebayo Ganiyu na cikin alkalan shari’ar zaben na 2023.

Wata majiya ta ce ana zargin Alkalan sun sa hannu a takardun CTC ne ba tare da karanta abin da ya kunsa ba, don haka dole za a hukunta su.

APC tayi nasara a Kano ko NNPP?

Da aka fitar da takardun dauke da kura-kurai, gwamnatin Kano ta ce ba a tsige ta ba, an rahoto Kwamishinan shari'a ya na cewa APC aka doke.

Ko kafin takardun hukuncin su fito, an ji sai da kotun ta dauki lokaci mai tsawo. Wasu su na ba alkalai uzuri aikin da ke kansu ne ya yi yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng