Kawu Sumaila: Sanatan NNPP Ya Fede Gaskiya a Shari’ar Zaben Gwamnan Jihar Kano
- Abdulrahman Kawu Sumaila ya soki yadda ake tafka da warwara wajen sauraro da yanke hukuncin zaben Gwamnan Kano
- Sanatan Kudancin Kano ya koka kan yadda ake neman karbe mulki daga hannun NNPP a mikawa wanda ya ce ya fadi zabe
- ‘Dan majalisar dattawan ya ce duk laifin da ake zargin Alkalai da aikatawa, ‘yan siyasa su ka fara nuna masu hanyar barna
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi dogon sharhi a game da abubuwan da ke faruwa a Kano saboda shari’ar zaben gwamna.
Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya tofa albarkacin bakinsa a wani bidiyo da aka fitar a dandalin Facebook a ranar Talatar nan.
Abdulrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta kudu a majalisar dattawa ya yi Allah-wadai da yadda shari’ar Kano ta kasance.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kawu Sumaila ya koka da shari'ar zaben Kano
Amma duk da tir da mutane su ke yi da Alkalan kotun korafin zabe da na kotun daukaka kara, Sanatan ya nemi ayi dogon nazari.
Sanata Kawu Sumaila ya ce ba Alkalai kadai za a jefa da zargin rashin gaskiya da yin ba daidai ba, a cewarsa akwai laifin ‘yan siyasa.
‘Dan majalisar yake cewa kafin a kai matakin da ake a yau, ‘yan siyasa da masu mulki ke nada wadanda za su zama alkalai tun farko.
'Yan siyasa su ka bata Alkalan zabe?
A bidiyon, ‘dan siyasar ya ce ba a duba cancanta a wajen zabo Alkalan kotun majistare, babban kotu da kuma kotun daukaka kara.
Har ila yau, jagoran na jam’iyyar NNPP ya zargi masu mulki da abubuwan rashin gaskiya a wajen zabe domin a samu mulki ido rufe.
Sumaila ya ce Alkalan da ake zargi da saida shari’a suna kallon yadda ‘yan siyasar kasar su ke yin magudi domin a ce sun lashe zabe.
Kano: Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna
A shari’ar Abba Kabir Yusuf v APC, Sanatan ya ce wanda ake kokarin damkawa mulkin jihar Kano ya san cewa bai yi nasara a zabe ba.
Sanatan Kudancin Kano ya nuna da farko ‘dan takaran APC ya rungumi kaddara har ya taya Abba Yusuf murna, sai yanzu labari ya canza.
Fitaccen ‘dan siyasar ya nuna takaicinsa kan yadda ake shari’ar gwamnan Kano, ya zargi jam’iyyu da tsaida ‘yan takara marasa farin jini.
'Dan adawar ya nuna ana neman hana majalisa yin aikinta a kasar, ya gargadi mutane kan hadarin goyon bayan zaluncin masu mulki.
Rudanin da aka kawo a shari'ar Kano
Ana da labari takardun CCT sun fito da kuskure, sun ce kotun daukaka ta rushe Hukuncin kotun karafin zabe a kan tsige Gwamnan Kano.
Bayanan da aka samu daga kotu a rubuce sun ce an karbi hujjojin Abba Kabir Yusuf, APC za ta biya shi N1m, sai daga baya aka ce tuntube aka yi.
Asali: Legit.ng