Daga Karshe, Gawuna Ya Taya Abba Gida-Gida Murna Nasarar Zaben Gwamna

Daga Karshe, Gawuna Ya Taya Abba Gida-Gida Murna Nasarar Zaben Gwamna

  • Bayan kai kawo, Gawuna ya fito ya taya Abba Kabir Yusif na murnar lashe zaɓen Kano
  • A baya dama Gawuna, yayi addu'ar idan zaɓen lashe zaɓen Kano alkairi ne Allah ya bashi.
  • Gawuna yayi addu'ar Allah yasa ya zama mai biyayya ga sabuwar gwamnatin da za'a kafa

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan daya gabata, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya taya zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusif murnar lashe zaɓen da akayi 18 ga watan Maris.

Ya aike da hakan ne ta wani ta wani gajeren saƙon WhatsApp wanda mai magana da yawun sa ya aikewa manema labarai a yau.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Karin Shekara: Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Ya Aike da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya Kafin Hawa Mulki

A faifan muryan, anjiyo Gawuna nayiwa Abba Kabir Yusif fatan alkairi gare da fatan Allah yasa ya zama shugaba nagari.

Gawuna yace, yanzu tunda dai INEC ta sanar da Abba a matsayin sahihin daya lashe zaben, APC daga nata tsagin tana nan tana aiki tukuru don ganin an canja lamarin.

Ya zargi INEC da bawa Abba satifiket na cin zaɓe, duk da akwai ƙorafi a gaban ta da suka shigar ba tare da sake tantance sakamakon zaben ba.

A cewar sa:

"Yanzu hukumar zaɓe ta tabbatarwa da Abba Kabir Yusif na NNPP zaɓe a 29 ga watan Maris, 2023.

"Kira ga masu goya mana baya, a baya ai munyi addu'a, munce idan alheri ne Allah ya bamu, idan kuma babu alheri , Allah ya canja mana da mafi alheri.

Gawuna ya ƙarkare da:

Kara karanta wannan

Jigon PDP Zai Cika Alkawarin Barin Najeriya Da Yayi Idan Tinubu Yaci Zaben Shugaban Kasa

"Wanda ya samu nasara, muna masa fatan Allah yasa ya zamto shugaba ba gari"

Daga nan sai yayi wa tarin magoya bayan sa godiya abiss yadda suka fito ƙwansu da ƙwarƙwatar su wajen zaben sa.

Ya roƙe su dasu zama masu ɗaukan ƙaddara.

Yayi addu'a akan shima Allah ya bashi daman ɗaukan ƙaddara da kuma biyayya ga sabuwar gwamnatin da za'a kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar

Online view pixel