PDP Ta Fitar Da Farashin Sayen Fom Din Takarar Gwamnan Edo, Ta Fara Shirin Zaben Fidda Gwani

PDP Ta Fitar Da Farashin Sayen Fom Din Takarar Gwamnan Edo, Ta Fara Shirin Zaben Fidda Gwani

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fitar da jadawalin ayyukan da za ta gudanar gabanin zaben gwamnan jihar Edo
  • Jam'iyyar za ta fara sayar da fom na tsayawa takarar gwamnan jihar a ranar 10 zuwa 16 ga Janairu, yayin da ranar 17 ga watan Janairu za ta zamo ranar rufewa
  • Ranar 22 ga watan Fabrairu ne jam'iyyar za ta gudanar da zaben fidda gwani na kujerar gwamna, kamar yadda jadawalin ya nuna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa ya fitar da jadawalin ayyukan da zai gudanar gabanin zaben gwamnan jihar Edo.

Jadawalin wanda babban sakataren jam’iyyar na kasa Umar Bature ya sanya wa hannu, an fitar da shi ne a ranar Alhamis, bayan kammala taron hadin gwiwa na kwamitin amintattu da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa a hedikwatarta da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun daukaka kara ta tsayar da ranar Juma’a don yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano

Jam'iyyar PDP
Kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP ya fitar da jadawalin ayyukan da zai gudanar gabanin zaben gwamnan jihar Edo Hoto: OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Nawa ne kudin sayen fom din tsayawa takarar?

A cewar jadawalin, babban taron jam’iyyar wanda a nan ne za a zabi dan takararta na gwamnan, zai gudana ne a ranar 22 ga Fabrairu, 2024, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, masu son tsayawa takarar gwamna za su samu fom din ne a kan Naira miliyan 21, yayin da matasa masu shekaru tsakanin 25 zuwa 30 za su samu rangwamen kashi 50 cikin 100 na kudin fam din takarar.

Ranakun fara rijista da ayyukan shuwagabanni

Bisa jadawalin ayyukan, rajistar tsofaffi da sabbin mambobi zai kasance a tsakanin 16 ga Nuwamba zuwa 7 ga Disamba, kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito.

Ranar 14 ga watan Disamba ita ce ranar karshe ta mika takardun rijistar gundumomi na jam'iyyar ga hukumar gudanarwa da hada-hadar kudi.

Kara karanta wannan

Dalilai 3 da suka sa Timipre Sylva na APC ya sha kaye a zaben gwamnan Bayelsa

Yayin da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar za su gana da hukumar tafiyar da ayyuka na kasa tsakanin 19 zuwa 20 ga watan Disamba.

Ranakun sayen fom da gudanar da zaben fitar da gwani

An tsara fara siyar da fom din nuna sha'awar tsayawa takara a dukkan kujeru a ranar 10-16 ga Janairu yayin da ranar 17 ga Janairu za ta kasance ranar karshe ta karbar fom din nuna sha'awar tsayawa takarar.

Kwamitin ayyuka na kasa zai gudanar da tantance masu neman kujerar gwamna a ranar 18 ga Janairu, 2024.

Ranar 22 ga watan Fabrairu ne jam'iyyar za ta gudanar da zaben fidda gwani na kujerar gwamna, yayin da aka tsayar da ranar 24 ga watan Fabrairu don daukaka kara kan zaben fidda gwani na gwamnan.

INEC ta sanya ranakun zaben gwamna a jihohin Edo da Ondo

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta ruwaito maku Hukumar zabe ta kasa (INEC), ta zabi ranakun da za ta gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Edo da kuma Ondo a shekara mai zuwa 2024.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar Gwamanan APC

A sanarwan da ta wallafa a shafinta na manhajar X, INEC ta sanya ranar 21 ga watan Satumba, 2024 a matsayin ranar da zata gudanar da zaben gwamna a jihar Edo da ke Kudu maso Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.