Tsige Gwamnan Kano: Bode George Ya Caccaki Hukuncin Kotun Daukaka Kara
- Bode George, jigo a jam’iyyar PDP, ya yi nazari kan hukuncin da kotu ta yanke na tsige Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano
- Ɗan siyasar na jihar Legas ya ce sam bai dace alƙalai su soke zaɓe tare da bayyana wanda ya lashe zaɓen ba
- A cewar George, hakan tare da cece-kucen da ke tattare da takardun CTC yana da matuƙar tayar da hankali domin ya saɓawa zaɓin masu zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Wani jigon jam’iyyar PDP, Bode George, ya caccaki matakin da alƙalai ke ɗauka na soke zaɓe da kuma bayyana waɗanda suka yi nasara, saɓanin abin da jama'a suka zaɓa.
Jigon PDP ya caccaki hukuncin korar Gwamna Yusuf
Ya yi wannan iƙirarin ne a lokacin da yake mayar da martani kan saɓanin da aka samu a takardun CTC na hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kan zaɓen gwamnan jihar Kano, wanda ya ce ba za a amince da shi ba, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, jigon a jam'iyyar PDP ya bayyana fargabar cewa an kusa fara kama karya idan ƴan Najeriya ba su aminta da ɓangaren shari'a ba.
George, wanda ya yi magana a madadin Majalisar Dattawan PDP na Legas a wani taron manema labarai a Legas a ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, ya bayyana halin da Kano ke ciki a matsayin wani shirin kawo hargitsi a ƙasa.
A kalamansa:
"Abin da ya kamata ɓangaren shari’a ya yi a shari’o’in siyasa shi ne yanke hukunci, idan kuma aka samu saɓani, sai a ba da umarnin a sake zaɓe ba tare da baiwa jam’iyyar A ko B nasara ba."
"Ba daidai bane a cire ikon da masu kaɗa ƙuri'a su ke da shi na zaɓar shugabannin siyasa sannan da ɓangaren shari'a ya gaya mana waɗanda suka lashe zaɓe. Wannan ba abu bane mai kyau ga Najeriya. Wannan ba abu bane mai kyau ga tsarin zaɓen mu. Ɓangaren shari'ar da ake haɗa baki da shi yana da hatsari."
Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano sun fito domin nuna adawa da hukuncin tsige shi da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke.
Magoyan bayan gwamnan sun gudanar da zanga-zangar ta lumana a wasu sassan birnin Kano, inda suka buƙaci a bar musu zaɓin da suka yi na gwamnan.
Asali: Legit.ng