Tsige Abba Gida Gida: An Kama Mutum 7 Kan Hukuncin Kotun Daukaka Kara, Cikakken Bayani
- Tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kotun Daukaka Kara ta yi na ci gaba da haifar da tashin hankali a jihar ta arewa
- A ranar Litinin, rundunar yan sanda ta bayyana cewa an kama kimanin mutane bakwai sakamakon bayanan sirri da aka samu cewa wasu na son tayar da tarzoma a jihar
- Usaini Gumel, kwamishinan yan sandan jihar, ya bayyana cewa jami'an rundunar sun tarwatsa kungiyoyi da suka badda kamanni a matsayin yan kasuwa
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Kano - Lamarin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a jihar Kano na ci gaba da haifar da fargaba a jihar ta Arewa maso Yamma yayin da yan sanda suka bankado wani yunkuri na tayar da tarzoma a jihar.
Wannan ya kasance ne yayin da rundunar yan sandan jihar ta bayyana cewa ta bankado shirin da wasu kungiyoyi ke yi na haddasa tarzoma a jihar kan hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta tsige gwamnan, jaridar Punch ta rahoto.
Yan sanda sun kama mutum bakwai da ke shirin tayar da tarzoma a Kano kan tsige Gwamna Yusuf
Usaini Gumel, kwamishinan yan sanda a jihar Kano, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, yana mai cewa zuwa yanzu rundunar ta kama mutum bakwai da ake zargi, sannan cewa za a gurfanar da su a gaban kotu, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gumel ya jaddada cewar kungiyar ta yi ikirarin cewa ta yan kasuwa ce, amma sun taru a wani wasu wurare a jihar, ciki harda kananan hukumomi yayin da ya bayyana cewa yan sanda na bisa kan lamarin.
Jawabinsa na cewa:
"Rahotannin sirri da muka samu ya nuna cewa wadannan da suka kira kansu da yan kasuwa suna amfani da addini wajen aiwatar da aika-aikarsu."
Yadda muka dakile tashin hankali a Kano, rundunar yan sanda ta magantu
Ya fada ma manema labarai cewa wasu yan Najeriya daga Bebeji, Wudin da sauran yankunan jihar sun sanar da yan sanda shirin kungiyoyin wadanda ke fakewa da karatun Al-Qur'ani.
A cewar shugaban yan sandan, jami'an rundunar sun farmaki wuraren sannan suka tarwatsa su daga taron.
Ya kuma nuna damuwa game da yunkurin kungiyar na tunzura jama'a a kan yan sanda ta hanyar yada jita-jitan cewa an ci zarafin mata yayin tarwatsa su.
Dan majalisa ya yi taron addu'a a Kano
A wani labarin, mun ji cewa Abdulmumin Jibrin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, ya ce kofar NNPP a bude take don yin hadaka ko maja da jam'iyyar APC.
Jibrin, na hannun daman Rabiu Musa Kwankwaso kuma jigo a jam'iyyar NNPP, ya ce jam'iyyar ba za ta damu da hada hanu da PDP ko LP ba.
Asali: Legit.ng