Shari’ar Zabe: Gwamnatin Abba Ta Tsokano Rigima Wajen Zargin APC da Ba Alkalai Cin Hanci
- Haruna Isa Dederi ya zargi jagororin APC da ba alkalan kotu cin hanci saboda a tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas bai ji dadin wannan zargi ba, ya nuna zai kai karar kwamishinan a kotu
- Babban lauyan gwamnatin na Abba Kabir Yusuf bai da niyyar janye kalaman da ya yi duk da wa’adin shugaban na APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kano - Shugaban jam’iyyar APC na reshen jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya yi barazanar kai karar Haruna Isa Dederi a gaban kotu.
Haruna Isa Dederi ya zargi jagororin APC da bada cin hanci a shari’ar zaben gwamnan Kano, Daily Trust ta ce hakan ya jawo fada.
APC za ta yi shari'a da Kwamishinan Abba a kotu
Shugaban APC ya ce idan har Barista Haruna Isa Dederi bai janye kalamansa nan da awanni 48 ba, lallai za su yi shari’a da shi a gaban kotu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Abdullahi Abbas ya bayyana haka ne a wata wasika da ya fitar tun ranar 23 ga Nuwamba 2023 wanda ta fito a yammacin ranar Lahadi.
APC ta ba alkalai cin hanci a shari'ar Kano?
Dederi wanda shi ne kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin Kano ya na zargin kudi sun yi aiki a shari’ar zaben gwamnan Kano.
A cewar Dederi, manyan APC sun ba alkalan kotun sauraron korafin zabe da alkalan kotun daukaka kara cin hanci domin a tsige NNPP a Kano.
Abbas ya ce zuwan Dederi gidan talabijin na kasa ya na cewa an yi hukuncin shari’ar Kano ta Zoom saboda katsaladan ne, sharri aka yi masu.
Shugaban na APC mai mulkin Najeriya ya ce kwamishinan shari’an ya kuma yi ikirarin Alkalan sun yi amfani da kudi wajen yin hukunci.
Kano: Gwamnatin Abba ta batawa APC suna?
Rahoto ya ce Abbas a wasikar da ya fitar jiya a Abuja, ya ce kalaman kwamishinan shari’an suna neman batawa ‘yan APC suna a jihar Kano.
A dalilin haka, Alhaji Abbas ya ce ana ta kiransa a waya domin jin gaskiyar zargin da ake yi masu na bada cin hanci domin su karbe mulki.
Duk da Abbas ya ce ana yi masa barazanar kisa har an yi masa barna a gida, Dederi ya nuna batun kai shi kara a kotun bai ba shi tsoro ba.
Da aka tuntube shi, masanin shari’an ya ce a kafar sada zumunta ya ji ana ta surutun.
Rigima kan shari'ar zaben Kano
Alkalai sun tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa zargin cewa shi ba ‘dan jam’iyyar NNPP ba ne da kuma sabawa ka’ida da dokokin zabe.
Amma ana da labari kwamishinan shari’a na Kano, Haruna Isa-Dederi ya hakikance kan cewa CTC ta nuna NNPP ta yi nasara a shari’ar zaben.
Asali: Legit.ng