Fiye da Shekaru 30 'Yan Najeriya Na Kira Na Don Neman Shugaban Kasa, Malamin Addinin Ya Magantu

Fiye da Shekaru 30 'Yan Najeriya Na Kira Na Don Neman Shugaban Kasa, Malamin Addinin Ya Magantu

  • Shugaban cocin Katolika a Sokoto, Mathew Hassan Kukah ya bayyana yadda fiye da shekaru 30 ake kiransa da tsaya wa takara a Najeriya
  • Kukah ya ce mutane su na yawan damunsa da ya fito neman takarar shugaban kasa inda su ke cewa zai dace da shugabancin kasar
  • Ya ce hatta kudin fom din takara sun ce za su biya masa amma shi ya sani ba zai zama shugaba mai kyau ba a Najeriya

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna – Shahararren Fasto a Najeriya, Mathew Hassan Kukah ya yi fatali da kiran da ake masa kan neman shugabancin kasar.

Kukah wanda shi ne shugaban cocin Katolika da ke Sokoto ya ce ya sani ba zai tsinana komai a matsayin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kano: Takardar CTC ta nuna Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Yusuf, Femi Falana

Kukah ya bayyana yadda mutane su ka yi ta damunsa ya tsaya neman takarar shugaban kasa
Kukah ya yi martani kan neman takarar shugaban kasa. Hoto: Mathew Hassan Kukah.
Asali: UGC

Mene Kukah ke cewa kan neman takara?

Faston ya bayyana haka ne yayin da ya ke jawabi a Kaduna inda ya ce mutane da dama sun yi ta damun shi ya tsaya takarar shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin addinin ya shafe shekaru 30 ya na jin ana ta kiraye-kiraye cewa ya fito neman shugabancin kasar, cewar Leadership News.

Ya ce:

“Mutane da yawa su na damu na kan neman takarar shugaban kasa fiye da shekaru 30.”

Wne martani ya yi kan neman shugabancin?

Ya kara da cewa:

“Oga, bari na gama da aikin coci tukun, saboda mutane da dama su na cemin za su biya min kudin siyan fom na takara.
“Su na cemin ba za ka biya ko sisi ba, mun san za ka yi kokari a shugaban kasa, amma na sani ba zan zama shugaba na kwarai ba saboda ba shi ake bukata ba.”

Kara karanta wannan

Bayan zama Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya fadi burin da ya rage masa a Duniya

Mathew ya ce ‘yan Najeriya ba shugabanni ma su kyau su ke nema ko ma su tsoron Allah ba, ya yi tambaya shin menene ma shugaba mai kyau?, cewar Daily post.

Ganduje ya gana da Jonathan

A wani labarin, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya saka labule da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje a Abuja.

Sai dai a lokacin sanar da ziyarar ta tsohon shugaban kasar da APC ta yi ba ta bayyana dalilin ziyarar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.