Shari’ar Kano: Gwamna Abba Ba Zai Maida Takardun Hukuncin Kotu ba Inji Lauyan NNPP
- Abba Kabir Yusuf ya ki yarda ya maida takardun shari’ar zaben gwamnan Kano zuwa ga kotun daukaka kara
- Lauyan da ya tsayawa Gwamnan, Wole Olanipekun ya ce doka ba ta ba kotun damar da ta wuce watanni 2 ba
- Wa’adin da aka ba kotun daukaka kara ya kare a makon jiya, Olanipekun ya ce sai dai kotun koli ta raba gardama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ki amincewa da bukatar kotun daukaka kara na dawo da takardun hukunci watau CTC.
Legit ta samu labari lauyan gwamnan jihar Kano a shari’ar da aka yi, Wole Olanipekun (SAN) ya fitar da wata wasika a matsayin martani.
Lokaci ya kure a shari'ar Kano?
A doguwar wasikar, Wole Olanipekun (SAN) ya ce kotun daukaka kara ba ta da hurumin gyara takardun hukuncin domin lokaci ya wuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan yake cewa a sashe na 285 (7) na kundin tsarin mulki, abin da dokar kasa ta ba kotun daukaka kara ta yi hukunci kwanaki 60 kacal ne.
Kano: Sai dai NNPP ta tafi kotun koli
Wadannan kwanaki sun kare daga ranar 18 ga watan Nuwamba, tun a makon jiya kenan, yanzu abin da NNPP ta ke so shi ne zuwa kotun koli.
The Nation ta ce kwararren lauyan ya ce yanzu ya ragewa kotun koli ta yanke hukuncin da ta ga ya fi dacewa bayan tuntuben alkalamin.
Kuskuren da aka samu ya jawo sabani da rabuwar kai tsakanin magoya baya a jihar Kano, har ta kai wasu su na cewa abin ya fi karfin kuskure.
Maganar Lauyan Abba Kabir Yusuf
"A kaddara a takardar hukuncin akwai wasu kura-kurai, na tuntuben alkalami ko makamancisu, mu na jawo hankalinku cewa lokaci ya kurewa kotun daukaka kara daga ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba 2023
Sai a kotun koli kurum za a duba maganar neman yin duk wani gyara.
Sannan sashe na 285 (7) na kundin tsarin mulki ya ce kotun daukaka kara ba za ta iya daukar wani mataki a shari’a ba bayan kwanaki 60."
-Lauyan NNPP a shari'ar Kano, Wole Olanipekun
Alkalai sun soke nasarar PDP a zaben Gwamnan Nasarawa, ana haka ne sai aka ji labari Abdullahi Sule ya ziyarci shugaban APC na kasa.
Tun tuni ake ta surutu a kan yadda kotu ta ke karbe jihohin adawa, ana damka su ga jam’iyyar APC, mun lura zargin ya na kara karfi a yanzu.
Asali: Legit.ng