Kano: Yayin da CTC Ta Tabbatar da Nasarar Abba Kabir, NNPP Ta Fadi Hanyar Warware Matsalar

Kano: Yayin da CTC Ta Tabbatar da Nasarar Abba Kabir, NNPP Ta Fadi Hanyar Warware Matsalar

  • Yayin da aka samu rikita-rikita a shari'ar zaben Kano, jami'yyar NNPP ta yi martani kan shari'ar
  • Kakakin jam'iyyar, Ladipo Johnson shi ya yi martanin a yau Laraba 22 ga watan Nuwamba yayin hira da gidan talabijin na Arise
  • Johnson ya ce abin takaici ne yadda Najeriya ta zubar da kimarta musamman a bangaren shari'ar kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jami'yyar NNPP ta yi martani kan rikita-rikitar da ke cikin hukuncin kotun daukaka a zaben gwamnan Kano.

Idan ba a manta ba a jiya Talata aka saki kwafin shari'ar ta CTC wacce ta sha bamban da hukuncin kotun daukaka kara, cewar Punch.

Jam'iyyar NNPP ta yi martani kan rikita-rikitar shari'ar zaben jihar Kano
NNPP ta yi martani kan rikicin hukuncin kotu a Kano. Hoto: Nasiru Gawuna, Abba Kabir.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a Kano?

Kara karanta wannan

Hujjojin da aka samu a takardun CTC sun nuna ba a tsige Abba ba – Gwamnatin Kano

Kotun daukaka karar ta sake tabbatar da rusa zaben Gwamna Abba Kabir na jihar Kano a ranar Juma'a 17 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin jam'iyyar, Ladipo Johnson ya ce za a sake duba yanayin shari'ar da kuma gyara ta a kotun koli, Daily Post ta tattaro.

Johnson ya bayyana haka a yau Laraba 22 ga watan Nuwamba yayin hira da gidan talabijin na Arise a Abuja.

Ya ce an samu bambanci tsakanin CTC da aka fitar a jiya na ainihi da kuma hukuncin kotun daukaka kara a ranar Juma'a.

Wane martani NNPP ta yi kan hukuncin Kano?

Ya ce:

"Wannan abin takaici ne ganin yadda muka zubar da mutuncinmu a bangaren shari'ar kasar.
"Abin ya kona min rai a matsayin masanin shari'a kuma lauya, abin da bacin rai ganin yadda muka tsinci kan mu."

Kara karanta wannan

Kano: Jigon NNPP ya tona asirin hanyar da APC ke bi don mayar da jihar karkashin ikonta saboda 2027

Johnson ya kara da cewa fitar kwafin CTC ba ta yi ma'ana ba ganin cewa kwanaki 14 kacal mai daukaka kara ke dashi don zuwa kotun gaba.

Ya ce ba su fitar da wannan ainihin kwafin ba sai bayan kwanaki biyar wanda hakan zai jawo matsala.

Abba Kabir ya sake mika kasafin kudi

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sake mika kwarya-kwaryar kasafin naira biliyan 24.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya mika biliyan 54 a watan Satumba da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel