Bayan Shari'ar Nasarawa, Kotu Ta Sake Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Gwamnan APC, Ta Ba da Dalili

Bayan Shari'ar Nasarawa, Kotu Ta Sake Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Gwamnan APC, Ta Ba da Dalili

  • Kotun daukaka kara ta sake raba gardama a shari'ar zaben gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya na jami'yyar APC
  • Kotun ta tabbatar da nasarar Inuwa Yahaya na jami'yyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe a jihar
  • Legit Hausa ta ji ta bakin hadimin Gwamna Inuwa, Yusuf Alyusra da jigon APC, Muhammad Auwal Akko

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Gombe.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya a matsayin halastaccen gwamnan jihar, Tribune ta tattaro.

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamna Inuwa a matsayin gwamnan jihar Gombe
Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Gombe. Hoto: Jibrin Barde, Inuwa Yahaya.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a Gombe?

Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Muhammad Jibrin Barde saboda rashin gamsassun hujjoji.

Kara karanta wannan

Kotu ta garƙame makusancin gwamnan PDP a gidan yari kan zargin ta'addanci da kisan rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan wanda dan jam'iyyar APC ne ya yi nasara a kotun sauraran kararrakin zabe inda ta tabbatar da shi a matsayin gwamnan jihar.

Barde na jam'iyyar PDP ya kalubalanci zaben ne da aka gudanar a watan Maris saboda tafka magudi da aka yi, cewar Daily Trust.

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu na kusa da gwamnan kan hukuncin.

Hadimin Gwamna Inuwa kan yada labarai na zamani, Yusuf Alyusra ya ce sun yi farin ciki da wannan nasara.

Ya ce daman wannan shi ne abin da al'ummar jihar su ka zaba.

A cewarsa:

"Mu na farin ciki da samun nasara a kotun daukaka kara.
"Kuma wannan daman shi ne bukatar al'ummar jihar Gombe kasancewar shine abin da mafi yawan al'ummar jihar su ka zaba.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Gwamnan APC ya tabo daliban firamare, ya raba musu kyautar N10,000 domin rage radadi

"Shi kuma wanda bai yi nasara ba mu na kiransa da ya rungumi kaddara ya kuma yi wa gwamnatin fatan alheri domin ci gaban jihar."

Har ila yau, jigon jam'iyyar APC a Gombe, Honarabul Muhammad Auwal Akko (Majikiran Gona) ya ce alkalan kawai sun tabbatar da abin da abin da al'umma su ka zaba ne.

Akko ya ce:

"Babu abin mamaki a hukuncin da kotun daukaka kara tayi bisa nasarar Alh Muhd Inuwa Yahaya, Gwamnan Gombe.
"Alkalan sun tabbatar da abin da al'ummar jihar Gombe su ka yi ne kawai lokacin zabe.
"Ta yaya mutumin da bai ci ko mazabarshi ba zai kai kara wai shi yaci zabe?"

Ya ce wannan dimaucewa ce kawai na faduwa zabe inda ya ba shi shawara ya rungumi kaddara ya bar wahalar da kansa.

Kotu ta tabbatar da nasarar Luggerewo a Gombe

Kun ji cewa, kotun daukaka kara ta tabbatar na nasarar kakakin Majalisar jihar Gombe, Abubakar Luggerewo a mazabar Akko ta Tsakiya.

Luggerewo wanda dan jam'iyyar APC ya yi nasara kan Bashir Gaddafi na jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.