Kano: Shehu Sani Ya Magantu Kan Takardar Kotu Da Ta Tabbatar Da Nasarar Abba Kabir Yusuf

Kano: Shehu Sani Ya Magantu Kan Takardar Kotu Da Ta Tabbatar Da Nasarar Abba Kabir Yusuf

  • Sanata Shehu Sani ya maganku kan takardar CTC da ta fita na hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke kan zaben gwamnan jihar Kano
  • Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya ce ya zama wajibi a yi taka tsan-tsan bayan da takardar CTC ta nuna cewa Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir
  • Sani ya yi nuni da cewa ba za a samu dorewar dimokuradiyya a Najeriya ba ma damar son zuciya zai rinka danne abin da doka ta tanadar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Tsohon sanatan mazabar Kaduna Ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce ya zama wajibi a yi taka tsan-tsan kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Yayin da CTC ta tabbatar da nasarar Abba Kabir, NNPP ta fadi hanyar warware matsalar

Sani ya ce takardar da ke yawo ta CTC na hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke, ya tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Shehu Sani ya magantu kan takardar CTC da ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba na Kano
Shehu Sani ya ce tilas ne ayi taka tsantsan da batun zaben gwamnan Kano. Hoto: Shehu Sani/Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Ya ce ba za a samu dorewar dimokuradiyya a Najeriya ba ma damar son zuciya zai rinka danne abin da doka ta tanadar, Legit ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shari'ar gwamnan Kano tana bukatar taka tsantsan - Shehu Sani

Tsohon dan majalisar dattawan ya bayyana hakan a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter) @ShehuSani, a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba.

Ya wallafa cewa:

"Kano; takardar CTC da ke yawo ta hukuncin Kotun Daukaka Kara ya nuna karara cewa gwamna mai ci shi ya ci zaben jihar."
"Lamarin tamkar gurneti ne wanda ya zama wajibi a sanya taka tsan-tsan. Ba za a samu dorewar dimokuradiyya a Najeriya ba ma damar son zuciya zai rinka danne abin da doka ta tanadar."

Kara karanta wannan

Tsohon Sanatan APC Ya Yi Allah Wadai da Kotu a Kan Tsige Gwamnonin PDP da NNPP

Hujjojin da ke dauke a takardun CTC

Takardun hukuncin kotu watau CTC da kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta fitar, ya jawo sabani tsakanin mutanen jihar Kano, Legit Hausa ta ruwaito.

An ji yadda bayanan da aka samu a rubuce su ka haddasa rudani tsakanin magoya bayan NNPP da APC game da shari’ar zaben gwamnan Kano.

Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnati, Haruna Isa-Dederi ya bayyana matsayarsu a sa’ilin da ya zanta da manema labarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.