Tsohon Mataimakin Gwamna da Wasu Jiga-jigan PDP 2 Sun Watsar da Lema, Sun Mara Wa Gwamnan APC Baya

Tsohon Mataimakin Gwamna da Wasu Jiga-jigan PDP 2 Sun Watsar da Lema, Sun Mara Wa Gwamnan APC Baya

  • Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun watsar da tafiyarta inda su ka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Neja
  • Daga cikin wadanda su ka sauya shekan akwai tsohon mataimakin gwamna, Ahmed Musa Ibeto
  • Sauran sun hada da tsohon mamban Majlalisar Wakilai, Ibrahim Ebo da tsohon kwamishinan Ruwa, Abubakar Azozo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Neja - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja, Ahmed Musa Ibeto da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC.

Ibeto wanda tsohon Ambasada ne a Najeriya da ke wakiltar Kudancin Afrika ya tsere a jam'iyyar yayin da ta ke fama da rikicin cikin gida, Legit ta tattaro.

Tsohon mataimakin gwamna da manyan PDP 2 sun sauya sheka zuwa APC
Jam'iyyar PDP ta samu rauni bayan jiga-jiganta sun koma APC a Neja. Hoto: @bago2027.
Asali: Twitter

Su waye su ka koma APC a Neja?

Kara karanta wannan

2027: NNPP ta amince da bukatar Atiku na yin hadaka, ta gindaya sharuda masu tsauri

Sauran wadanda su ka watsar da jam'iyyar akwai Ibrahim Ebo tsohon mamban Majalisar Wakilai da tsohon kwamishinan Ruwa, Abubakar Azozo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibeto ya ce ya samu karfin gwiwar koma wa APC ne saboda ayyukan alkairi na Gwamna Umaru Bago na jihar Neja.

Ahmed Ibeto ya bayyana haka ne a jiya Talata 21 ga watan Nuwamba a sakatariyar jam'iyyar da ke Minna a jihar, Tribune ta tattaro.

Ya ce Bago ya kawo ayyukan ci gaba da raya kasa inda ya ce jam'iyyar gida ne a wurinshi kuma ya dawo.

Mene dalilin komawarsu APC a Neja?

Ya kara da cewa irin kawo dauki da Gwamna Bago ke yi ga marasa karfi na daga cikin abubuwan da su ka ja hankalinsu zuwa APC.

Tsohon Ambasadan ya ce akwai wasu 'yan jam'iyyar PDP da dama su ke tafe su ma don ba da gudunmawarsu ga jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Kujera za ta haddasa sabuwar rigima tsakanin Wike da gwamnoni a Jam’iyyar PDP

Da yake martani, hadimin gwamnan a bangaren siyasa, Mohammed Nma Kolo ya ce irin shugabancin Bago shi ke jawo hankalin mutane zuwa APC.

Kolo ya ce sun karbi da dama kuma su na sauraran wasu wadanda su ka gama shirin sauya sheka zuwa APC saboda irin mulkin adalcin Bago.

Kansilolin PDP 19 sun koma APC a Kaduna

A wani labarin, Kansilolin jam'iyyar PDP 19 daga kananan hukumomi 23 sun sauya sheka zuwa APC.

Kansilolin sun sauya shekan ne ganin irin ayyukan alkairi da Gwamna Uba Sani na jihar ke aiwatarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel