Rikicin PDP: Yadda Atiku da Obi Za Su Kayar da Tinubu a Zaben 2027

Rikicin PDP: Yadda Atiku da Obi Za Su Kayar da Tinubu a Zaben 2027

  • Atiku Abubakar da Peter Obi sun samu shawara kyauta kan yadda za su kayar da Tinubu a zaɓen 2027
  • Richard Ngene a wata tattaunawa da Legit.ng ya shawarci Atiku da ya marawa Peter Obi baya a zaɓen 2027
  • A cewarsa idan Atiku ya yi hakan zai sanya su iya ƙwace mulki daga hannun jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Biyo bayan hukuncin kotun ƙoli, masu sharhi kan harkokin siyasa sun yi ta tofa albarkacin bakinsu kan yadda Atiku Abubakar da Peter Obi, masu rike da tutar jam’iyyar PDP da Labour Party (LP) a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, za su samu mafita a nan gaba.

A wata hira da Legit.ng ta yi da Honorabul Richard Ngene, jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon mai taimaka wa gwamnan Enugu, ya bayyana cewa mafita mai kyau ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa shi ne ya marawa Obi baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

Bayan Kano, Mataimakin Shugaban APC ya faɗi kujerar gwamnan da zasu ƙwace a arewa

An shawarci Atiku da Peter Obi
An ba Atiku da Peter Obi shawara kan yadda za su kayar da Tinubu a zaben 2027 Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi
Asali: Twitter

Kotun koli ta yi watsi da ƙarar da Atiku da Obi suka shigar kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ya tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Biyo bayan hukuncin kotun, Atiku mai shekaru 81, wanda a baya ya nuna sha’awarsa ta sake tsayawa takara a zaɓen 2027, ya bukaci haɗewar jam’iyyun adawa domin kawar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Dalilin da zai sa Atiku ya janye aniyarsa yin takara a 2027

Sai dai Ngene ya bayyana cewa zai fi kyau Atiku ya goyi bayan aniyar Obi[ na zama shugaban ƙasa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 maimakon ya sake yin takara a zaɓe mai zuwa.

Jigon na APC ya kuma tabbatar da cewa Atiku zai yi babban kaso a gwamnatin Obi idan har ya marawa tsohon gwamnan na jihar Anambra baya.

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: An ba gwamnan APC wa'adin sa'o'i 72 ya mika mulki ga mataimakinsa

A cewar Ngene:

"Abin da Atiku yake bukata shine ya marawa Peter Obi baya a PDP kuma zai samu damar zaɓar mataimakin shugaban ƙasa kamar Tinubu yadda ya tsayar da Osinbajo takara a 2015."

LP Ta Yi Watsi da Kiran Atiku Abubakar

A wani labarin kuma, jam'iyyar Labour Party (LP) ta yo watsi da kiran da Atiku Abubakar ya yi na su haɗe domin yaƙar Tinubu a zaɓen 2027.

Jam'iyyar ta bayyana cewa babu wani batun haɗaka da za ta yi da Atiku Abubakar, saɓanin jita-jitar da ake ta yaɗawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel