Ba Na Tsoron a Sake Zabe, Gwamna Dare na Jihar Zamafara
- Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara ya nuna karfin gwiwar cewa shine zai yi nasara a zaben da za a sake fafatawa tsakaninsa da Bello Matawalle
- Lawal ya ce ko gobe aka ce ayi zabe a karamar hukumar Maradun, a shirye suke su lashe zaben
- Dandazon al'ummar jihar Zamfara sun tarbi gwamnan yayin da ya dawo jihar daga ziyarar aiki da ya kai kasar Côte d’Ivoire
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya nuna karfin gwiwar yin nasara a zaben da kotun daukaka kara ta yi umurnin sakewa a jihar.
Lawal ya ce mutanen jihar sun yarda da shi a matsayin wanda zai tafiyar da harkokin jihar, cewa baya tsoron a sake zabe, jaridar Punch ta rahoto.
Ku tuna cewa kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta bayyana zaben gwamnan jihar a matsayin wanda bai kammala ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne bayan an ayyana Lawal, dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Sai dai kuma, dan takarar gwamnan jam'iyyar APC, Bello Matawalle, ya kalubalanci sakamakon zaben gwamnan na ranar 18 ga watan Maris, a kotun zabe amma aka yi watsi da hukuncin saboda rashin hujja.
Amma kuma, kotun dauka karar ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba sannan ta umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ta gudanar da sabon zabe a kananan hukumomi biyu.
Dandazon jama'a sun tarbi gwamnan Zamfara
Da dawowarsa a ranar Litinin, daga wani ziyarar aiki da ya kai kasar waje, gwamnan ya samu tarba daga magoya bayansa a lokacin da ya isa garin Gusau, babban birnin jihar.
Ya je Abidjan, kasar Côte d’Ivoire, tare da sauran gwamnonin arewa maso yamma shida inda suka gana da jami'an Bankin raya Afrika a lokacin da kotun daukaka karar ta yanke hukunci.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, kakakin gwamnan, Sulaiman Idris, ya bayyana taron mutanen da suka tarbi gwamnan a matsayin shaida da ke nuna karbuwar gwamnatinsa.
Idris ya ce,:
“Gwamnatin Lawal ta samu gagarumin goyon baya daga al’ummar Zamfara, wadanda suka nuna soyayyar su a matsayin mubaya'a.
“Yayin da Gwamna Dauda Lawal ya dawo Zamfara daga ziyarar aiki da ya kai Abidjan, ya samu tarba daga jama’a da ba a taba ganin irinsa ba.
"Ayarin motocin gwamna Lawal sun samu tarba daga dimbin jama'a tun daga karamar hukumar Tsafe har zuwa Gusau, babban birnin jihar."
Daga nan sai mai magana da yawun gwamnan ya nakalto ubangidan nasa yana shaidawa magoya bayansa a sakatariyar jam’iyyar PDP na jihar cewa al’ummar jihar sun amince da shugabancinsa.
An tattaro cewa ya sha alwashin yin aiki tukuru don girmama wannan yarda da suka yi da shi.
"Ko gobe ne zabe a shirye muke mu je karamar hukumar Maradun", Lawal Dare
Kamar yadda jaridar Daily Post ta rahoto, Gwamna Lawal ya ce Allah ya rigada ya nada shi Gwamnan jihar, yana mai ba da tabbacin cewa hakan ne zai ci gaba da kasancewa, duk da kulla-kullan da yan APC da sauran makirai za su yi.
Ya ce:
“Ba ma tsoron sake yin zabe. Al'ummar Zamfara sun damka mana amanar kuri'unsu.
“Mun shirya kuma muna kyautata zaton cewa ko da gobe za a yi zaben, a shirye muke mu je karamar hukumar Maradun.
"Mun jajirce sosai wajen aikin cetonmu, kuma babu wani tangarda da zai hana mu azama da mayar da hankali."
Gwamnan Zamfara ya yi hasashen nasara
A baya mun ji cewa gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ce ya shirya tsaf domin tukarar ƙarishen zaɓen da kotun ɗaukaka kara ta umarta a hukuncin da ta yanke.
Gwamnan na PDP ya jaddada cewa jam'iyyar adawa APC na kishi da hassadar ɗumbin ayyukan ci gaban da ya kawo Zamfara cikin watanni biyar da hawa mulki.
Asali: Legit.ng