Matawalle Vs Lawal: Gwamnan PDP Ya Faɗi Wanda Zai Samu Nasara a Zaben da Za a Ƙarisa a Zamfara

Matawalle Vs Lawal: Gwamnan PDP Ya Faɗi Wanda Zai Samu Nasara a Zaben da Za a Ƙarisa a Zamfara

  • Dauda Lawal ya ce yana da kwarin guiwar shi zai doke ƴan adawa a zaben da Kotun ɗaukaka ƙara ta yi umarnin a sake a Zamfara
  • Gwamnan na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa APC na hassada ne da ɗumbin ayyukan ci gaban da ya zuba a jihar cikin watanni 5 kaɗai
  • A makon jiya Kotun ta rushe nasarar Gwamna Lawal kana ta umarci INEC ta shirya zabe a kananan hukumomi guda uku

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ce ya shirya tsaf domin tukarar ƙarishen zaɓen da kotun ɗaukaka kara ta umarta a hukuncin da ta yanke.

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
Gwamna Lawal na Zamfara ya nuna kwarin guiwa samun nasara, ya ce APC na hassada Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamnan na PDP ya jaddada cewa jam'iyyar adawa APC na kishi da hassadar ɗumbin ayyukan ci gaban da ya kawo Zamfara cikin watanni biyar da hawa mulki.

Kara karanta wannan

Jigon PDP kuma Lauya ya feɗe gaskiya kan hukuncin kotun daukaka ƙara na tsige gwamnan arewa

Dauda Lawal ya yi wannan kalamai ne yayin da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa a Sakateriyar PDP da ke Gusau, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lawal ya bayyana cewa Allah ne ya zabe shi ya zama gwamna, inda ya kara da cewa zai ci gaba da rike mukaminsa duk baƙin cikin ƴan adawa.

Idan baku manta ba kotun ɗaukaka ƙara ta rushe nasarar Gwamna Lawal, inda ta umarci hukumar zaɓe INEC ta shirya zaɓe a kananan hukumomi uku, Maradun, Birnin-Magaji, da Bukkuyum.

Zan ci gaba da yi wa Zamfarawa aiki - Lawal

Amma Lawal ya jaddada cewa ‘yan adawa ba za su ɗauke masa hankali su hana shi kara kawo ci gaba a faɗin jihar Zamfara ba.

Gwamnan ya kuma yi kira ga ɗaukacin magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar da su kwantar da hankalinsu kuma su bi doka da oda, su guji tada yamutsi.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Atiku Abubakar ya maida martani mai zafi kan tsige gwamnonin arewa biyu

Ya bayyana kwarin guiwar cewa shi ne zai sake samun nasara a zaben da za a ƙarisa a waɗannan kananan hukumomi guda uku, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Ya ƙara da yabawa magoya bayan PDP bisa goyon baya da karfafa masa gwiwa ta hanyar addu’o’in da suke yi wanda ya ce ya kara masa himma wajen tafiyar da al’amuran jihar.

Bwala ya caccaki hukuncin tsige Gwamnan Filato

A wani rahoton kuma Jigon PDP, Daniel Bwala ya caccaki matakin tsige gwamnan jihar Filato da Kotun ɗaukaka ƙara ta yi ranar Lahadi.

A wata hira, tsohon kakakin kwamitin kamfen shugaban ƙasa na PDP ya ce ba a taɓa soke zaɓe saboda wani ya ƙi bin umarnin kotu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel