"Lafin Ka Ne": Hadimin Tinubu Ya Fadi Abu 1 da Obasanjo Ya Yi da Ya Sa Kasar Nan a Mawuyacin Hali
- Fadar shugaban ƙasa ta yi nuni da cewa Obasanjo ya taka rawar gani wajen ɗora ƙasar nan kan irin tsarin dimokuraɗiyyar da take kai a lokacin mulkinsa na soja
- Fadar shugaban ƙasa ta yi wannan ikirarin ne a lokacin da take mayar da martani kan sukar dimokuraɗiyya irin ta ƙasashen yamma da Obasanjo ya yi a baya-bayan nan
- Fadar shugaban ƙasar ta nuna cewa, idan Obasanjo ya yi imani da buƙatar sauyi, ya kamata ya ba da shawarar a dawo da tsarin da ƙasar take a kai kafin zuwan sojoji a shekarar 1966
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Fadar shugaban ƙasa, Abuja - Gwamnatin tarayya ta shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta dora alhakin halin da dimokuraɗiyyar Najeriya ke ciki a kan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.
Hadimin Tinubu ya mayar wa Obasanjo martani
Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya jaddada cewa dimokuradiyyar da ake a ƙasar nan tana da alaƙa da shugabancin Obasanjo a lokacin da yake mulkin soja da na farar hula.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ku tuna cewa Obasanjo ya bayyana cewa dimokuraɗiyya ba ta aiki a Afirika saboda tilasta ta a kan mutane.
Ya ce ya kamata Afirika ta yi abin da ya kira "Dimokuaɗiyyar Afirika" a maimakon dimokuraɗiyyar ƙasashen Yamma.
Da yake mayar da martani, Onanuga ya bayar da hujjar cewa zargin da Obasanjo ya yi ya zama abin ban mamaki domin ya taka muhimmiyar rawa wajen yarda da tsarin dimokuraɗiyyar a shekarar 1979 da kuma daga baya a lokacin da yake shugabancin ƙasar daga 1999 zuwa 2007.
A wata hira da jaridar The Punch da aka buga a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, Onanuga yayin da yake mayar da martani kan kalaman na Obasanjo, ya bayyana cewa:
"Obasanjo ya kamata ya sani shi ya kawo wannan dimokuraɗiyyar cikin Najeriya. Shi ne ya sa muka karɓe ta a 1979, tabbas ya gano tana da tsada da rashin dacewa lokacin da ya yi mulkin mu na tsawon shekara takwas, har ma ya so ya ƙara wasu shekara huɗu"
"Don haka, yadda yake surutai, kamar yanzu ya fi wayau bayan ya bar ofis."
Obasanjo Ya Magantu Kan Zaɓen 1998
A wani labarin kuma, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda jam'iyyar PDP ta sha kaye a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Ogun a shekarar 1998.
Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa jam'iyyar ta sha kaye ne saboda ƙin amincewa da ba hukumar zaɓe ta INEC cin hanci.
Asali: Legit.ng