‘Dan Majalisa Ya Fito a Bidiyo Ya Cika Baki APC Za Ta Karbe Gwamna a Hannun PDP a Kotu
- Yusuf Adamu Gagdi ya ce za su karbe mulkin jihar Filato daga hannun jam’iyyar PDP idan an je kotun koli
- ‘Dan majalisar na Pankshin/Kanke/Kanam ya jawowa jam’iyyarsa ta APC abin magana da barambar da ya yi
- Gagdi shi ne shugaban kwamitin harkokin sojojin ruwa a majalisa, su ne jagororin jam’iyyar APC a jihar Filato
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Yusuf Adamu Gagdi yana shan suka daga wajen mutane saboda an ji shi a bidiyo ya na na maganganu kan shari’ar zaben Filato.
Hon. Yusuf Adamu Gagdi mai wakiltar Pankshin/Kanke/Kanam a majalisar wakilan tarayya yana ganin jihar Filato za ta dawo hannun APC.
A bidiyon da wani ‘dan jarida, Chuks Akunna ya wallafa Twitter, an ji ‘dan majalisar yana takamar PDP za ta rasa mulkin Filato a kotun koli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman Adamu Gagdi kanz aben Filato
"Mun je kotun daukaka kara. Kuma kotun karshe ita ce kotun koli. Kuma za mu hadu a nan.
A (kotun kolin) ne za mu san wadanda su ka sani, kuma za su su san wadanda mu ka sani."
- Hon. Yusuf Adamu Gagdi
APC za ta yi karfa-karfa a tsige PDP?
A lokacin da Hon. Gagdi wanda tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin Filato ne ya ke maganar, ana ji wasu su na ta jinjina masa.
Sai dai mutane da ke amfani da dandalin Twitter sun yi Allah-wadai da kalaman da su ka fito daga bakin shugaban kwamitin na sojojin ruwa.
Wani @DeinmoweiEzi ya ce Gagdi ya fadi haka ne saboda ya san alkalan kotun koli za su karbi cin hanci domin a fifita jam’iyyar APC mai-ci.
“Ina ji wa bangaren shari’a kunya. Ya na barazanar yi wa shari’a katsalandan a fili saboda hakan ya zama al’ada”
– Grace Habiba
Dogo Nanzing ya ce:
“Abin takaici ne.”
Karimjeffabdul ya rubuta:
“Mai neman zama shugaban majalisar wakilai kenan.”
Shi kuwa N.I Timothy ya ce APC ta kunyata a zaben 2023, amma ta dage sai ta karbe mulki da karfi da yaji.
Kotu ta sake tsige Gwamnan PDP
Kwanakin baya labari ya zo cewa kotun daukaka kara ta tsige Gwamna Caleb Mutfwang bisa zargin PDP da sabawa doka.
Dama can shugaban PDP na kasa na rikon kwarya, Iliyasu Umar Damagun, ya soki hukuncin da aka yi, ya ce an yi masu son-kai.
Asali: Legit.ng