Kano: Sheikh Khalil Ya Fadi Abin Da Zai Faru a Kotun Koli, Ya Bai Wa Kwankwaso, Abba Kabir Shawara
- Babban shehin malami a jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya yi martani kan yadda shari'ar zaben Kano za ta kasance
- Ibrahim Khalil ya ce alamu ya nuna cewa 'yan Kwankwasiyya ba su da nasara amma ya na shawartarsu da su daukaka kara
- Ya ce ba ya na karya musu gwiwa ba ne amma abin a fili ya ke tun da sun sha kaye a hawa na farko da na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce zai yi wahala jam'iyyar NNPP ta yi nasara a kotun koli.
Shehin malamin ya ja hankalinsu da su daukaka kara don samun damar lokacin da za su tsara barin gidan gwamnati, cewar Leadership Hausa.
Mene Sheikh Khalil ke cewa kan shari'ar Kano?
Sheikh Khalil ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sadarwa a jiya Litinin 20 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce bai kamata zuciyarsu ta karye ba wurin zuwa kotun koli inda ya ce hakan ba karya musu gwiwa ba ne illa gaskiyar a fili ta ke.
Ya kara da cewa tun da shari'ar farko ba su yi nasara ba, ta biyu ma babu nasara, ya kamata su je kotun gaba don samun lokacin tsara shirin barin mulki.
Wane shawara Sheikh Khalil ya bayar kan shari'ar Kano?
Ya ce:
"Muna jan hankalinsu su daukaka kara don samun lokacin tsara gwamnatinsu su fita lafiya.
"Ba muna karya musu gwiwa ba ne amma abu ne a bayyane a fili dole su karbi gaskiya tun da hawa na farko da na biyu ba su yi nasara ba, dole su je kotun koli.
"Kira ga 'yan Kwankwasiyya kada su fito su yi rigima ko su yi fada da ta da hankali, da kuma sake shiri idan su na jin sun iya to sun hadu da gwanaye."
Ibrahim Khalil ya shawarci jam'iyyar APC da cewa tun da shari'ar ta gano sun fi kusa da gaskiya, kada su ce za su yi ramuwar gayya da cin zarafi.
Halin da ake ciki bayan hukuncin kotu a Kano
A wani labarin, bayan yanke hukuncin kotu a Kano, mutane sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum bayan hukuncin.
Wannan na zuwa ne bayan kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin karamar kotu na kwace kujerar Abba Kabir na jam'iyyar NNPP.
Asali: Legit.ng