Abba: Saboda Kwankwaso Aka Huro Wuta Ana So a Tunbuke Ni Daga Mulkin Kano
- Abba Kabir Yusuf ya yi jawabi a wajen wani taro da Rabiu Musa Kwankwaso ya kira bayan zuwansa Kano a karshen makon jiya
- Gwamnan na jihar Kano ya alakanta yunkurin tsige shi a kotu da goyon baya da biyayyar da yake yi wa madudun Kwankwasiyya
- Duk da jam’iyyar APC ta kama hanyar karbe nasarar Abba Gida Gida a zaben 2023, Gwamnan ya nuna har yanzu ba su taba karaya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Abba Kabir Yusuf ya ce matsalolin da yake fuskanta a yau a kotu a kan shari’ar zabe saboda alakarsa da Rabiu Musa Kwankwaso ne.
Mai girma Gwamnan Kano ya yi jawabi a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki a tafiyar Kwankwasiyya da aka shirya a yammacin ranar Lahadi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi dogon jawabi cikin dare wanda shi ne karon farko tun bayan da kotun daukaka kara ta tsige shi daga kan mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya yi kira ga 'Yan NNPP a Kano
Gwamnan da aka fi sani da Abba Gida Gida ya nuna bai ki ya rasa komai saboda tsabagen biyayyar da yake yi wa Rabiu Kwankwaso a siyasa ba.
A jawabinsa, Abba ya yi kira ga jiga-jigan jam’iyyar NNPP da su ka kara karfafa magoya bayansu, kamar jagoran na su, ya ce ba za su karaya ba.
Biyayyar Abba Gida Gida ga Kwankwaso
"Kamar yadda na yi bayani, za mu cigaba da aiki a karkashin jagorancinsa (Kwankwaso) kuma mu yi abin da ya dace.
Amma dole mu gode masa (Kwankwaso), dole mu kara gode masa, kuma dole mu fada masa, mu mu na alfahari da shi.
Idan duniya ta ce ba za ta ba mu wani abu ba saboda mu na yi masa (Kwankwaso) biyayya, Allah ya raka taki gona.
- Abba Kabir Yusuf
Taron siyasa a gidan Kwankwaso
Mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, shugaban majalisar dokoki, Ismail Falgore da Abdulmumin Jibrin Kofa sun halarci taron.
Kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto a yau, manyan gwamnatin Kano, kwamishinoni da kuma jagororin NNPP duk su na wajen taron.
Asali: Legit.ng