Sabuwar Rigima Ta Ɓalle a Hedkwatar Jam'iyyar PDP Ta Kasa, An Nemi Mambobin NWC Su Yi Murabus
- Sabuwar matsala ta kunno kai yayin da masu zanga-zanga suka mamaye hedkwatar jam'iyyar PDP a Abuja
- Gungun masu zanga-zangar sun nemi dukkan mambobin kwamitin gudanarwa NWC na ƙasa su yi murabus
- Sun zarge su da rashin iya aiki da kuma taimaka wa wajen darewar jam'iyyar PDP zuwa ɓangarori daban-daban
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gungun masu zanga-zanga sun mamaye hedikwatar babbar jam'iyyar adawa, Peoples Democratic Party (PDP) da ke birnin tarayya Abuja.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, masu zanga-zangar sun bukaci dukkan shugabannin jam'iyyar PDP na ƙasa watau mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) su yi murabus.
Tawagar mutanen sun ɓarke da zanga-zangar ne ƙarƙashin kungiyar "PDP National Back Up" kuma suka durfafi Wadata Plaza, inda hedkwatar PDP take a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun buƙaci muƙaddashin shugaban APC na ƙasa, Umar Damagun da sauran abokan aikinsa na NWC na kasa su gaggauta yin murabus.
Masu zanga-zangar sun sanya tufafin fari da baƙi, ɗauke da rubutun, "Dole mambobin kwamitin gudanarwan PDP na ƙasa NWC su yi murabus."
Meyasa suke son a rushe NWC?
Da yake jawabi ga yan jarida, shugaban tawagar masu zanga-zangar, Salau Olusola, ya zargi NWC-PDP da cin amana da zagon ƙasa.
A cewarsa, "Shugabannin PDP na ƙasa ne suka ja wa jam'iyyar rashin nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023."
“Nyeson Wike da sauran mambobin G-5 sun ci amanar PDP a zaben 2023, duk da haka NWC da Damagum ke jagoranta ya ki ladabtar da su. Bisa haka kawuna suka rabu, ba zamu lamurci wannan ba."
"Sauran dalilan mu sun hada da rigingimun cikin gida da ake ta fama da su, bangaranci, ko rashin hadin kai a PDP ya haddasa neman a samu sabbin shugabanni."
Da aka tambaye su ko me za su yi idan mambobin NWC suka ki yin murabus, ya bayyana cewa “Mun shirya bin matakan shari'a kuma gobe za a aiko musu da sammaci."
DHQ ta yi bayanin harin da aka kaiwa Gwamna Buni
A wani rahoton kuma Hedikwatar tsaron ƙasa ta bayyana yadda sojoji suka daƙile harin da yan ta'adda suka kaiwa ayarin Gwamna Buni na jihar Yobe.
A ranar Asabar da ta gabata ne yan ta'adda suka farmaki ayarin motocin gwamnan na APC a hanyar zuwa Damaturu.
Asali: Legit.ng