Fadar Shugaban Kasa Ta Fayyace Ainihin Sababin Tsige Abba da Gwamnan Filato a Kotu
- Mai taimakawa shugaban kasa wajen dabaru da yada labarai ya wanke zargin da ake jifan Bola Ahmed Tinubu da su
- Bayo Onanuga ya ce sabawa ka’idojin zabe da kundin tsarin mulki ya jawo NNPP da PDP su ka rasa kujerunsu a kotu
- Bayan samu nasara a zaben 2023, ana zargin Bola Tinubu ya sa hannu APC ta karbe kujerar wasu Gwamnonin adawa
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Fadar shugaban kasa ta fitar da jawabi a game da abin da ya sa gwamnonin jihohin Filato da na Kano su ka rasa kujerunsu a kotu.
A cikin kwanaki hudu, kotun daukaka kara ta tsige Gwamna Caleb Muftwang da Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan yin watanni biyar a ofis.
Akwai hannun Tinubu a shari'o'in zabe?
Bayo Onanuga wanda Hadimi ne ga Bola Ahmed Tinubu ya fitar da jawabi a shafinsa na Twitter, inda ya yi kokarin wanke shugaban Najeriyan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu suna zargin akwai hannun Mai girma Bola Ahmed Tinubu wajen hukuncin da aka yi.
Mista Bayo Onanuga ya ce masu sukar shugaban kasa saboda an tsige Caleb Mutfwang sun manta da abin da ya faru da APC a zaben 2019.
Filato: Abin da ya faru da APC a zaben 2019
"A 2019, duka wadanda aka zaba a APC a jihar Zamfara, tun daga Gwamna zuwa ‘yan majalisar jiha da tarayya sun rasa mukamansu saboda APC ba ta gudanar da sahihin zaben tsaida gwani ba.
PDP ba ta koyi darasi da abin da ya faru a tarihi ba, su ka maimaita kuskuren saba dokan, su ka yi amfani da kwamitin rikon kwarya wajen zaben tsaida ‘yan takaran, duk da umarnin kotu.
Ku zargi PDP da matsalar da aka samu, ba APC, Alkalai, INEC ko shugaba Tinubu ba."
- Bayo Onanuga
Meyasa kotu ta tsige Abba Kabir Yusuf?
"Rashin bin ka’idojin zabe da tsarin mulki shi ne silar soke zaben Gwamnan Kano, Abba Yusuf.
An tsige Abba ne bisa doka, kuma na yi imani duk mu na so kasarmu ta rika yin aiki da doka."
- Bayo Onanuga
Kotu ta tsige 'Yan majalisan Filato
Hon. Happiness Akawu ta bar majalisar dokokin jihar Filato a sakamakon tsige ta da kotu ta yi kamar yadda aka samu labari a yammacin Lahadi.
Kujerar Hon. Rimvjat Nanbol ta koma hannun Daniel Ninbol wanda ya yi takara a LP a Langtang, sannan kotu ta tsige Hon. Agbalak Adukuchill.
Asali: Legit.ng