Zamfara: APC ta mika sunayen ‘yan takara ga INEC
Biyo bayan hukun kotun daukaka kara da ke Sokoto, jam’iyyar APC mai mulki ta mika sunayen ‘yan takarar ta daga jihar Zamfara ga hukumar zabe mai zaman kan ta domin a fafata da su a zabukan shekarar nan.
Da yak e tabbatar da hakan ga manema labarai a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja, gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya ce APC ta bayar da sunayen ‘yan takarar ne bisa dogaro da hukuncin da kotun ta yanke a jiya, Laraba.
“Mun yi matukar farinciki da wannan hukunci na kotu, hakan ya tabbatar da cewar mun gudanar da zabukan cikin gida bisa ka’ida,” a cewar Yari.
Babatunde Ogala, mai bawa APC shawara a harkokin shari’a, ya bayyana cewar jam’iyyar ta aika sunayen ‘yan takarar jihar Zamfara ga INEC domin ta shigar da su cikin jerin ‘yan takarar da za a fafata da su a zabukan kujeru daban-daban da za a yi.
A jiya ne Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar wata kotun daukaka kara da ke jihar Sokot ta warware hukuncin da wata babbar kotu a jihar Zamfara ta yanke a kan hana hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) karbar sunayen ‘yan takarar jam’iyyar APC na kujeru daban-daban a zaben da za a yi cikin watan Fabarairu da Maris.
Hukuncin kotun ya share wa jam’iyyar APC hanyar shiga domin a fafata da ita a dukkan zabukan shekarar nan da za a fara ranar Asabar mai zuwa.
DUBA WANNAN: Rashin jituwa: Shekarau ya yi karin haske a kan alakar sa da Buhari
Kotun mai alkalai uku ta yi warware hukuncin kotun farkon ne biyo bayan janye karar da Aminu Jaji, wanda ya shigar, ya yi.
INEC ta kafe kan cewar ba zata karbi sunayen ‘yan takarar APC daga jihar Zamfara ba saboda gaza kammala zabukan cikin gida a kan lokaci da jam’iyyar ta yi.
Hukumar zaben ta tsaya tsayin daka a kan matakin da ta dauka bayan wasu hukunci ma su cin karo da juna da kotun jihar Zamfara da wata ta tarayya su ka zartar a rana guda.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng