Bayan Kujerar Gwamna, Kotu Ta Sake Korar Wasu Karin ‘Yan Majalisan PDP 3 a Jihar Filato

Bayan Kujerar Gwamna, Kotu Ta Sake Korar Wasu Karin ‘Yan Majalisan PDP 3 a Jihar Filato

  • Jam’iyyar APC ta tashi da karin kujerun ‘yan majalisar dokoki a jihar Filato bayan hukuncin kotun daukaka kara
  • Alkalai sun kora Hon. Happiness Akawu da Hon. Agbalak Adukuchill daga majalisa, APC ta maye gurabensu
  • Jam’iyyar LP ta samu kujerar Langtang ta Arewa maso tsakiya a sakamakon soke nasarar Hon. Rimvjat Nanbol

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A ranar Lahadi, kotun daukaka kara mai zama a garin Abuja ta yi hukunci a kan shari’ar zaben majalisar dokokin jihar Filato.

Blueprint ta ce a karshen zaman da aka yi, Alkalan kotun daukaka kara sun tsige wasu ‘yan majalisan jihar Filato da ke karkashin PDP.

'Yar majalisa
'Yar majalisar Filato da aka tsige a PDP Hoto: Happiness Mathew Akawu
Asali: Facebook

PDP ta barar da kujerun Majalisar Filato

Kara karanta wannan

Tsohon Sanatan APC Ya Yi Allah Wadai da Kotu a Kan Tsige Gwamnonin PDP da NNPP

Mai shari’a Williams-Dawodu ya jagoranci shari’ar inda ya zartar da hukuncin da ya raba jam’iyyar PDP da kujeru uku a majalisar dokoki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan hukunci ya ci Hon. Happiness Akawu, aka maye gurbinta da Hon. Yakubu Sanda, ‘dan takaran APC zai wakicli mazabar Pengana.

A Rukuba/Irigwe, Dawodu da sauran abokan aikinsa sun tunbuke Hon. Agbalak Adukuchill Ibrahim, su ka ba Kawo Bako Ankala nasara.

LP ta samu kujerar Majalisa a Filato

Rahoton ya ce an kori Hon. Rimvjat Nanbol na PDP daga majalisa, kujerar Langtang ta koma ga ‘dan takaran LP, Daniel Ninbol Listic.

Alkalan kotun daukaka karan sun ce jam’iyyar PDP ta yi watsi da umarnin da babban kotu ta bada a 2020 na shirya zaben shugabanni.

Filato: Yadda aka ba APC da LP nasara

Rashin fitar da shugabanni a reshen Filato ya kawo kotu ta ce jam’iyyar hamayyar ba ta da ikon tsaida ‘yan takara a babban zaben bana.

Kara karanta wannan

Wasu sun tsinke da lamarin Tinubu da Kotu ta tsige gwamnonin adawa 3 a kwana 4

Daily Trust ta ce kotu ta yi amfani da sashe na 177c na kundin tsarin mulkin 1999 da sassa na 80 da 82 na dokar zaben shekarar 2022.

Kotu ta ba PDP umarnin ne a shari’a mai lamba PLD/J304/2020 tsakanin Bitrus B. Kaze da wasu mutum 11 da PDP da wasu mutane 24.

Sakataren yada labaran PDP, Debo Ologunagba ya shaidawa manema labarai cewa tun farko sun san haka za ayi masu a shari’ar Filato.

Sanata ya soki hukuncin zaben Filato

A rahoton nan, an ji cewa tsohon Sanata a Kaduna, Shehu Sani ya ce kotu tana neman zama makarar da ake birne damukaradiyya.

Shehu Sani ya zargi Alkalai da fito da wasu dabaru domin a karbe mulki daga hannun gwamnoni kamar yadda aka yi a Kano da Filato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng