Zamfara: Babban Malami Ya Bayyana Jam'iyyar da Za Ta Yi Nasara Bayan Kotu Ta Umurci a Sake Zabe
- Babban Fasto a Najeriya ya yi hasashen abin da zai faru a jihar Zamfara bayan kotu ta rusa zaben jihar
- Fasto Elijah Ayodele ya bayyana cewa nasarar ta na ga PDP inda ya ce babu abin da zai faru na tashin hankali kan sake zaben
- Faston ya bayyana haka ne a jiya Juma'a 17 ga watan Nuwamba a shafinsa na Twitter inda ya ce Matawalle zai sha kaye a zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Shahararren Fasto, Elijah Ayodele ya ce ko da an sake zabe a kananan hukumomi uku, Gwamna Dauda Lawal ne zai yi nasara.
Fasto Ayodele ya bayyana haka ne a shafin Twitter a jiya Juma'a 17 ga watan Nuwamba.
Mene Fasto Ayodele ke cewa kan zaben Zamfara?
Ya ce umarnin da kotun daukaka kara ta yi na sake zabe a kananan hukumomi uku ba wata babbar matsala ba ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayodele ya ce wannan nasarar za ta wuce ne ga jam'iyyar PDP mai mulkin jihar yayin da Bello Matawalle na APC zai sha kaye, Legit ta tattaro.
Matawalle wanda yanzu shi ne karamin Ministan Tsaro ya yi takara a jam'iyyar APC a zaben da aka gudanar.
Wane shawara ya bai wa Gwamna Dauda Lawal?
Faston a cikin wani faifan bidiyo da ya yada wanda Legit ta gano ya ce:
"A jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal bai kamata ya yi bacci ba, amma ba wata babbar matsala ba ce a hukuncin kotun.
"Nasarar ta PDP ce, ya kamata su fara tsare-tsare don ganin sun yi nasara a zaben."
Ya kara da cewa:
"Babu wani abu a cikin sake zaben, sake zaben kawai wata sanarwa ce, don haka ba wata matsala."
Kotu ta rusa zaben Gwamna Dauda na Zamfara
A wani labarin, kotun daukaka kara ta ayyana zaben gwamnan jihar Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba.
Kotun ta umarci sake zabe a wasu kananan hukumomi uku da ke jihar saboda tafka kura-kurai da aka yi yayin gudanar da zaben a watan Maris.
Asali: Legit.ng