Rigima Sabuwa: An Ba Gwamnan APC Wa'adin Sa'o'i 72 Ya Mika Mulki Ga Mataimakinsa

Rigima Sabuwa: An Ba Gwamnan APC Wa'adin Sa'o'i 72 Ya Mika Mulki Ga Mataimakinsa

  • Rikicin da ya dabaibaye kujerar mulkin jihar Ondo ya ƙara zafafa sosai inda ake cigaba da matsin lamba ga gwamna
  • Jam’iyyar adawa ta PDP ta bi sahun ƙungiyoyin masu fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya wajen yin kira ga Gwamna Rotimi Akeredolu da ya koma bakin aikinsa
  • An bai wa gwamnan wa'adin kwanaki uku na komawa ofis ko ya miƙa mulki ga mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gamayyar shugabannin jam’iyyar adawa da gamayyar ƙungiyoyin jam’iyyar PDP Forever Initiative, sun ba gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu wa'adin sa’o’i 72 ya miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa.

Ƙungiyar ta bayyana bukatar hakan ne a wata ganawa da manema labarai a Abuja, inda ta bayyana fargaba kan yadda gwamnan ya dade yana jinya saboda matsalolin da suka shafi lafiya, inda ta ce hakan ya janyo tsaiko a shugabanci tare da kawo cikas ga harkokin mulkin jihar.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya bayyana hanya 1 da za a magance matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas

An taso Akeredolu a gaba sai ya ba da mulki
Gwamna Akeredolu ya samu wa'adin sa'o'i 72 kan ya mika mulki ga mataimakinsa Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi
Asali: Facebook

Kodinetan PDP Forever Initiative na ƙasa, Hon. Obande Gideon Obande, ya fayyace cewa damuwarsu ba ta shafi iya mulkin Gwamna Akeredolu ba amma halin rashin lafiyar da yake ciki a halin yanzu, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An buƙaci Gwamna Akeredolu ya yi biyayya ga tsarin mulki

Ƙungiyar ta jaddada buƙatar gwamnan ya bi tanade-tanaden kundin tsarin mulki tare da miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa domin tabbatar da ɗorewar harkokin mulki a jihar.

Ƙungiyar ta yi gargaɗin mamaye gidan gwamnatin jihar Ondo idan har aka yi watsi da wa'adin, inda ta zargi jam'iyyar APC da gazawar jagoranci a matakin jiha da tarayya.

Sun zargi wasu ƴan jam'iyyar da kawo cikas ga ayyukan da suka rataya a kan mataimakin gwamnan jihar da kuma ta’azzara al’amura a jihar.

A yayin da suke jaddada aniyarsu ta inganta shugabanci na gari da bin tsarin mulki, ƙungiyar ta yi kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya, ba tare da la'akari da siyasa ba, da su goyi bayan ƙoƙarinsu na tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin shugabanci.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan Majalisa ɗaya tilo da take da shi a jihar Arewa, ya koma APC

Wa'adin da ƙungiyar PDP Forever Initiative ta bayar ya ƙara ta'azzara tabarbarewar siyasa a jihar Ondo, lamarin da ya haifar da rashin tabbas kan ko Gwamna Akeredolu zai bi bukatunsu ko kuma lamarin zai ƙara ta'azzara.

Malamin Addini Ya Hango Matsala a Ondo

A wani labarin kuma, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya bayyana cewa ya hango gagarumin rikicin siyasa a jihar Ondo.

Babban faston ya bayyana cewa ya hango cewa lafiyar Gwamna Akeredolu ba za ta daidaita ba, sannan addu'a ce kawai za ta hana a tsige mataimakin gwamna Licƙky Aiyedatiwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng