'Jarabawa Ce, Gwamna Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotun da Ta Rusa Zabenshi, Ya Sha Alwashi

'Jarabawa Ce, Gwamna Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotun da Ta Rusa Zabenshi, Ya Sha Alwashi

  • Gwamnan jihar Zamfara ya yi martani kan hukunci kotun daukaka kara a jiya Alhamis 17 ga watan Nuwamba
  • Gwamna Dauda Lawal ya ce wannan wata jarabawa ce ta lokaci kadan kuma za su samu nasara a hukuncin gaba
  • Wannan na zuwa ne bayan kotun ta rusa zaben kananan hukumomi guda uku tare da umarnin sake zabe a wuraren

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara – Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi martani kan hukuncin kotun daukaka kara a jiya Alhamis.

A jiya Alhamis 16 ga watan Nuwamba kotun daukaka kara ta ayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammala ba.

Gwamna Dauda ya yi martani kan hukuncin kotun daukaka kara na zaben gwamna
Gwamna Dare ya sha alwashin kwato kujerarshi. Hoto: @DaudaLawalD.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a Zamfara?

Kara karanta wannan

“Muna ta addu’a”: Ta hannun damar Ganduje ta yi martani ga hukuncin kotu da ta tsige Abba Gida Gida

Kotun ta rusa zaben kananan hukumomi inda ta ba da umarnin sake zabe a wadannan wurare, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Bukuyun da Maradun da kuma karamar hukumar Birnin-Magaji.

Yayin martaninshi, Gwamna Lawal ya roki mutanen jihar da su kwantar da hankalinsu kan wannan hukunci, cewar Leadership.

Wane martani Dauda ya yi kan hukuncin?

Lawal ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sulaiman Idris ya fitar a yau Juma’a 17 ga watan Nuwamba a Gusau babban birnin jihar.

Ya ce:

”Alkalan kotun guda uku sun bayyana cewa zaben jijar Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba.”
“Ina kira ga mutane su kwantar da hankalinsu, lauyoyinmu su na duba yanayin shari’ar don ganin an dauki matakin da ya dace.

Gwamnan ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya bayan kotun daukaka kara ta tsige Abba Gida-Gida daga matsayin gwamnan Kano

“Wannan hukuncin kotun ba komai ba ne illa jarabawa ta dan lokaci kadan kuma mu na da tabbacin bukatun mutane za su yi nasara a hukuncin gaba.
“Mun sha bakar wahala kafin samun wannan nasara, amma ina ba ku tabbacin mun shirya tsaf don kwato kujerarmu.”

Kotu ta rusa zaben gwamnan jihar Zamfara

A wani labarin, kotun daukaka kara ta yi hukunci kan zaben gwamnan jihar Zamfara a jiya Alhamis 17 ga watan Nuwamba.

Kotun ta rusa zaben kananan hukumomin jihar guda uku inda ta umarci hukumar zabe da ta sake zabe a wadannan wurare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.