‘Yan Sanda Sun Haramta Murna Ana Shirin Yanke Hukunci Kan Shari’ar Zaben Gwamna

‘Yan Sanda Sun Haramta Murna Ana Shirin Yanke Hukunci Kan Shari’ar Zaben Gwamna

  • A yau Juma’a ne Alkalan Kotun daukaka kara za su zartar da hukunci a kan shari’ar zaben Gwamnan jihar Bauchi
  • Mai girma Bala Abdulqadir Mohammed zai san matsayinsa bayan kotun da ke zama a Abuja ya yi hukunci an jima kadan
  • Air Marshall Sadique Abubakar mai ritaya ya shigar da kara a kotu, ya na ikirarin shi ya lashe zaben Gwamna a 2023

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - A yau ranar Juma’a, Kotun daukaka kara da ke zama a garin Abuja za ta yanke hukunci a kan shari’ar zaben gwamnan jihar Bauchi.

Punch ta fitar da rahoto cewa a yau ne kotun daukaka kara za ta yanke hukunci a shari’ar Bala Abdulqadir Mohammed da Sadique Abubakar.

Kara karanta wannan

Shari’ar Zabe: Gwamnatin Abba Gida-Gida ta yi muhimmin kira kafin a shiga Kotu

Shari’ar Zaben Gwamna
Kotu za ta yi hukunci a shari'ar Gwamnan Bauchi Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Shari'ar zaben Gwamnan Bauchi

Air Marshall Sadique Abubakar mai ritaya ya na kalubalantar zaben Bala Mohammed a matsayin Gwamna, ya kai kara a kotun zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan rashin dacen da ya yi a kotun sauraron korafin zaben Bauchi, ‘dan takaran na APC ya tunkari kotun daukaka ko zai dace wannan karon.

Yau za ayi hukuncin Kano da Bauchi

Majiyoyi sun tabbatar da cewa kotu ta tsaida 17 ga watan Nuwamba 2023 a matsayin ranar da za a zartar da hukunci a shari’ar ta PDP v APC.

Babban kotun za ta tabbatar da hukuncin Mai shari’a P. T. Kwahar ko kuwa ta rusa shi, hakan ya jawo jam’iyyu da masoya su ke fatan nasara.

'Yan sanda sun ja kunnen APC da PDP

Ana haka sai ga sanarwa daga Kakakin rundunar ‘yan sandan reshen jihar Bauchi, Ahmed Waki, a kan haramtawa magoya baya murnar hauka.

Kara karanta wannan

'Inconclusive': Kotu ta ayyana zaben gwamnan Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba, za a sake zabe

The Guardian ta ce Ahmed Waki ya shaidawa manema labarai ba za su amince da wannan ba.

Sanarwar ta ce Kwamishinan ‘yan sandan Bauchi ya karfafa tsaro saboda gudun tsageru su yi barna bayan kotu ta zartar da hukunci a yau.

Sufiritandan ‘yansandan ya ce ba za su amince da toshe tituna, amfani da wuta da abubuwan fashewa da sunan murnar nasara a kotu ba.

Rundunar ‘yan sandan ta yi gargadi kan amfani da miyagun kalamai da za su iya fusata jama'a, an yi alkawarin hukunta masu taurin-kai.

'Yan sanda sun dauki matakai a Kano

An samu irin wannan labari daga Kano da aka ji ‘Yan sanda da sauran jami’an tsaro suna tabbatar da tsaro yayin da kotu za ta zartar da hukunci.

A safiyar Juma'a za a kawo karshen shari’ar APC da NNPP kan zaben Kano a kotun daukaka kara, daga nan kuma sai a garzaya zuwa kotun koli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng