Majalisar Jihar Arewa Ta Rage Wa'adin Shugabannin Kananan Hukumomi

Majalisar Jihar Arewa Ta Rage Wa'adin Shugabannin Kananan Hukumomi

  • Majalisar dokokin jihar Taraba ta sabunta dokar da ta shafi wa'adin shugabannin kananan hukumomi
  • Majalisar ta rage wa'adin shugabannin kananan hukumomin daga shekaru uku zuwa shekaru biyu a jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin zaben shugabannin kananan hukumomin a jihar a ranar Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - Majalisar dokokin jihar Taraba ta sabunta dokar wa'adin shugabannin kananan hukumomi a jihar.

Majalisar ta rage wa'adin shugabannin ne daga shekaru uku da ake yi zuwa shekaru biyu kacal a kan mukami, The Nation ta tattaro.

Majalisar Taraba ta rage wa'adin shugabannin kananan hukumomi a jihar
Majalisar jihar Taraba ta yi gyaran fuska a dokar kananan hukumomi. Hoto: KefasAgbu.
Asali: Twitter

Mene dalilin gyaran fuska ga dokar kananan hukumomi?

Daya ya ke amsa tambayoyi kan dokar, shugaban kwamitin yada labarai a Majalisar, Nelson Len ya ce dokar za ta fara nan take.

Kara karanta wannan

'Inconclusive': Kotu ta ayyana zaben gwamnan Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba, za a sake zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Honarabul Nelson ya ce dokar za ta fara aiki ne kan sabbin shugabannin kananan hukumomi da za a tabbatar da su a ranar Asabar 18 ga watan Nuwamba.

Ya ce:

"Dokar mai sauki ce, ta na magana ne kan zaben shugabannin kananan hukumomi da kuma wa'adin da za su yi a kan mulki."

Wsu hanyoiy aka bi don gyaran fuska ga dokar?

Nelson ya ci gaba da cewa:

"Garanbawul ne daga wa'adin shekaru uku zuwa shekaru biyu, mu na son gyara wa saboda ya zama doka ga wadanda za a zaba."

Nelson ya ce dalilin da ya sa aka yi zaman a boye shi ne saboda ma'aikatan Majalisar na kasa baki daya su na yajin aiki.

Ya ce an bi dukkan hanyoyin da su ka dace wurin tabbatar da gyaran dokar kananan hukumomin a Majalisar.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasar Malawi Chakwera ya haramtawa kansa da ministocinsa fita waje

Majalisa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 3

A wani labarin, Majalisar jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi guda uku saboda fita kasar waje ba tare da izinin zartarwa ba.

Wadanda dakatarwar ta shafa sun hada da Honarabul Mubarak Ahmad daga karamar hukumar Birniwa da ke jihar.

Sauran sun hada da Honarabul Rufai Sunusi na karamar hukumar Gumel da Honarabul Umar Baffa daga karamar hukumar Yankwashi duk a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.