Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana

Babbar Jam'iyyar adawa a Najeriya, Peoples' Democratic Party PDP a yau Laraba, 25 ga Mayu, 2022 take gudanar da zaben fidda gwanin yan takaran gwamna a zaben 2023.

Za'a gudanar da wannan zabe ne a jihohi 32 a fadin tarayya

Ku bibiyi shafin nan don samun bayanai kai tsaye kan zabuka.

Dauda Lawal ya kashe zaben fidda gwanin Zamfara

Dauda Lawal, jigon PDP a jihar Zamfara ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan jihar a zaben da ya gudana ranar Laraba.

Shugaban kwamitin zaben, Adamu Maina, ya sanar da cewa Lawal ya samu kuri'u 431, yayinda Ibrahim Shehu ya samu kuri'u 5.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa yan takara uku, Abubakar Nakwada, Wadatau Madawaki da Ibrahim Shehu sun janye saboda zargin magudi.

Mallam Ubandoman Sokoto ya lashe zaben fiddan gwanin PDP a Birnin Shehu

Tsohon Sakataren gwamnatin jihar Sokoto, Mallam Saidu Umar, ya zama dan takaran gwamnan jihar Sokoto karkashin jam'iyyar PDP.

Shugaban kwamitin zaben, Dr Tom Zakari, wanda ya jagoranci zaben yace Umar ya samu kuri'u 695 cikin deleget 755, rahoton TheNation.

Sauran yan takaran sun janye masa.

Sun hada da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Mukhatar Shagari da shugaban PDP na jihar, Bello Aliyu Goronyo.

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Asali: UGC

Barista Caleb Mutfwang ya lashe zaben fidda gwanin Plateau

Barista Caleb Mutfwang ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan jihar Plateau karkashin jam'iyyar PDP.

TheNation ta ruwaito cewa Muftwang, wanda shine tsohon shugaban karamar hukumar Mangu ya samu kuri'u 252, inda ya lallasa sauran yan takara 15.

An kammala zaben ne da safiyar yau Alhamis, 26 ga Mayu, 2022.

Sauran yan takaran Chief Wungak Kefas ya samu 113; Mr Dapal Alfred Ali 92; Chief Dauda Wuritka Gotring 88; Dr. Mazadu Dader Bako 3; Chief Jonathan Sunday Akuns16; Chief Gushop Jerry Danjuma 6; Amb. Hirse Bagudu Mutle 1; Chief Satu Jatau Jewin 9; Nde David Shikdu Parradang 4; Prof. Shedrack Best Gaya 4; Mr. Alexander Bitrus Landan 02; Brig. Gen. John Sunday Sura Rtd 03 da Mr. Ephraim Lenka Dewa 0

Davematics Ombugadu ya lashe zaben jihar Nasarawa

Tsohon dan majalisar wakilan tarayya, David Ombugadu, ya lashe zaben fiddan gwanin gwamnan Nasarawa karkashin jam'iyyar PDP.

Shugaban kwamitin zaben, Bature Musa, ya sanar da cewa Ombugadu ya samu kuri'u 247, yayinda wanda ke biye masa Janar Nuhu Angbazo ya samu kuri'u 203.

Ombugadu
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Asali: Twitter

Isa Ashiru Kudan ya lashe zaben Kaduna

Burin Shehu Sani na zama sabon gwamnan jihar Kaduna a 2023 ba zai cika ba, a sakamakon rashin nasarar da ya yi a zaben fitar da gwani.

‘Dan siyasar ya tabbatar da wannan a Twitter da asuban ranar Alhamis. Sani ya taya wanda ya yi nasara murna, ya yabawa wadanda suka ba shi kuri'arsu.

Tsohon Sanatan ya sha kashi a hannun Honarabul Isah Ashiru Kudan a zaben fitar da ‘dan takarar da aka yi a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, 2022.

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Asali: UGC

Mohammed Abacha ya lashe zaben fidda gwanin PDP na gwamna a Kano

Mohammed Abacha, dan marigayi tsohon shugaban kasa, Sani Abacha, ya lashe zaben fidda dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Kano.

Jami'ar zabe, Barista Amina Garba, ta ayyana Mista Abacha a matsayin wanda ya lashe zabe bayan ya samu kuri’u 736 wajen kayar da babban abokin hamayyarsa, Sani-Bello wanda ya samu kuri’u 710, PM News ta rahoto.

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana Hoto
Asali: Getty Images

Jandor ya lashe zaben fidda gwanin Legas

Shugaban kungiyar Lagos4Lagos Olajide Adediran (Jandor) ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan jihar Legas karkashin jam'iyyar PDP.

Shugaban kwamitin zaben, Emmanuel Ogidi, yace Jandor ya samu kuri'u 679 inda ya lallasa abokin hamayyarsa David Vaughan, wanda ya samu kuri'u 20.

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Farfesa Uche Ikonne ya lashe zaben jihar Abia

Tsohon shugaban jami'ar jihar Abia, Farfesa Uche Ikonne, ya zama dan takaran kujerar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP a zaben 2023.

Kamfanin dillancin labarai ta ruwaito cewa Farfesan ya lashe zaben da kuri'u 468.

Mr Lucky Igbokwe wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 45, sannan Ngozi Merenge ta samu kuri'u 5.

Ibrahim Kashim ya yi nasara a zaben jihar Bauchi

Ibrahim Kashim ya ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jihar Bauchi karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023.

NAN ya ruwaito cewa Kashim kadai ne mutumin da ya fito takarar kujerar a jihar.

Shugaban kwamitin zaben, Hassan Grema, ya sanar da hakan bayan kammala zaben ranar Laraba a Bauchi.

Ya ce mutum 656 ne suka kada kuri'a.

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Jajari ya lashe zaben jihar Borno

Mohammed Jajari ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jihar Borno karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa Jajari ya samu kuri'u 487 inda ya kayar da Mohammed Imam wanda ya samu kuri'u 362.

Baturen zaben, Abdulrahman Bobboi, ya alanta Jajari matsayin wanda yayi nasara.

Jajari
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Fasto Umo Enor ya lashe zaben jihar Akwa Ibom

Fasto Umo Enor ya zama dan takarar kujeran gwamnan jihar Akwa Ibom karkashin jam'iyar PDP.

Mutum 1,018 ne suka kada kuri'a a zaben.

Enor ne zabin gwamna mai ci, Udom Emmanuel.

Tsohon mai magana da yawun Atiku ya lashe zaben jihar Ogun

Tsohon mai magana da yawun Alhaji Atiku Abubakar, Segun Sowunmi, ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan jihar Ogun na jam'iyyar PDP.

Taron zaben ya gudana ne a OPIC, Abeokuta, birnin jihar.

Sowunmi ya lallasa hadimin El-Rufa'i, Jimi Lawal da Ladi Adebutu.

Ya smau kuri'u 554, yayinda Jimi Lawal ya samu 30 kuma Ladi Adebutu ya samu 15.

Baturen zaben, Abayomi Daniel ya alantashi matsayin wanda yayi nasara.

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Asali: Twitter

Kakakin majalisar dokokin Benue ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan Jihar

Kakakin majalisar dokokin Benue, Titus Uba, ya zama zakaran zaben tsayar da gwani na jam'iyyar PDP a jihar. Ya lallasa mataimakin gwamnan jihar

Titus ya lashe zaben ne da ya gudana a filin kwallin Aper Aku dake Makurdi, birnin jihar, rahoton Channels TV.

Ya samu kuri'u 731 kuma ya kayar da mataimakin gwamnan jihar wanda ya samu kuri'u 81.

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

'Dan Sule Lamido ya lashe zaben fidda gwanin yan takarar gwamnan Jigawa

Mustafa Lamido, dan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya lashe zaben fidda gwanin yan takarar gwamnan a Jigawa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Baturen zaben fidda gwanin, Isah Ahmed, ya bayyana hakan lokacin ya sanar da sakamakon zaben ranar Laraba a Dutse.

Isah Ahmed ya sanar da cewa Mustafa Lamido ya samu kuri'u 829 cikin mutum 832 da suka ka'da kuri'a yayinda abokin hamayyarsa Saleh Shehu bai samu kuri'a ko guda ba.

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Asali: Twitter

Dan sanda ya suburbudi dan jarida wajen zaben Ibadan, kungiyar yan jaridar sun kai kararsa

Kungiyar yan jaridar Najeriya, shiyyar jihar Oyo ta kai karan jami'in dan sanda da ya suburbudi dan jarida dake kawowa jaridar TheNation rahoto wajen zaben fidda gwanin PDP a Ibadan.

Jami'an yan sanda sun lallasa dan jaridan mai suna Yinka Adeniran, har ya yada masa riga.

Tsohon Minista Labaran Maku ya janye daga zaɓen fidda gwanin PDP a Nasarawa

Tsohon Ministan yaɗa labarai, Labaran Maku, ya sanar da janye wa daga tseren neman tikicin PDP a zaɓen gwamnan jihar Nasarawa bayan an fara zaɓen fidda gwani.

Vanguard ta rahoto cewa Maku ya ce bayan faɗaɗa neman shawari daga abokansa da makusanta, ya yanke shawarin janye wa daga nema takarar gwamnan.

Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

An dage zaben fitdda gwani da ke gudana a jihar Neja, biyo bayan wata zanga-zanga da ta barke.

Zaben da aka shirya gudanarwa a yau Laraba ya koma Alhamis bayan zanga-zangar da hudu daga cikin biyar da ke takara suka tayar.

an fara samun matsala ne yayin da hudu daga cikin biyar din suka nuna rashin gamsuwa da jerin sunayen deliget-deliget da za su kada kuri'a

Yan takara uku sun janye a jihar Legas

Mutum uku cikin mutum 6 masu takaran kujerar gwamna a jihar Gwamna sun janye.

Sune Deji Doherty, Otunba Olarenwaju Jim-Kamal da Ade Dosumu.

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintri ya lashe zaben fidda gwani

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintri ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya samu jimillar kuri’u 663 daga cikin 668 da aka ka'da

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya janye daga zaben a Abia

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijan tarayya, Eyinnaya Abaribe, ya janye kansa daga cikin masu takara a zaben fidda gwanin dan takara gwamnan PDP a jihar Abia.

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Asali: Facebook

Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara ya janye daga takarar gwamna a PDP

Gabanin zaben fidda gwani na gwamna na jam'iyyar PDP, tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara Barista Mahdi Aliyu Gusau ya fice daga takarar.

Channels Tv ta rahoto cewa, Mahdi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakatarensa Umar Aminu a Gusau babban birnin jihar Zamfara ranar Laraba.

Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Kai tsaye: Yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar PDP ke gudana
Asali: Facebook

Sanata Ekweremadu ya janye daga zaɓen fidda gwani na PDP

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, ya janye daga zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP a Enugu.

Darakta Janar da ƙungiyar kamfen ɗinsa, Charles Asogwa, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito

Online view pixel