Abubuwa Za Su Sukurkucewa Dino Melaye, APC Ta Kawo Hujjar Daure ‘Dan Takaran PDP
- Jam’iyyar APC ta na ganin ya kamata jami’an tsaro su yi maza-maza su cafke ‘Dan takaran PDP a zaben Kogi watau Dino Melaye
- Kingsley Fanwo a matsayinsa na Darektan yakin neman zaben ‘dan takaran APC ya zargi abokin adawarsu a Kogi da yi wa INEC kutse
- Tun farko APC ta na ganin Dino Melaye ba zai je ko ina wajen neman Gwamna ba, ta ce akwai alamar tambaya game da kan kuri’unsa
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kogi - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Kogi ta yi kira ga jami’an tsaro su gaggauta cafke Dino Melaye saboda ana zargin ya aikata laifuffuka.
The Nation ta rahoto APC mai mulki tana mai cewa Sanata Dino Melaye da bakinsa ya fadawa duniya ya aikata laifuffuka ta yanar gizo.
Jam’iyyar ta APC ta ce ‘dan takaran PDP a zaben Kogi ya tona kan shi ne da aka yi hira da shi a gidan talabijin game da zaben da aka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta yi wa Dino Melaye martani
Darektan labarai da hulda da jama’a na kwamitin kamfen Ahmed Usman Ododo, Kingsley Fanwo ya bukaci jami’an tsaro su cafke Dino.
Kakakin kwamitin yakin yake cewa ‘dan takaran jam’iyyar hamayyar ya saukaka aikin jami’an tsaro domin ya amsa laifinsa da bakinsa.
A yayin da yake jawabin godiya a Lokoja, an rahoto Fanwo ya na jifan Melaye da rashin kunya da yi wa shafin yanar gizon INEC kutse.
Dino ya ce ya kamata ‘ya ‘yan shugaban hukumar INEC su ji kunyan zaben da aka gudanar a jihar Kogi, amma APC ba ta bar shi haka ba.
AIT ta rahoto Fanwo ya ce ‘ya ‘yan Dino ba za su yi alfahari da borin da mahaifinsu ya rika yi a zauren majalisar tarayya a shekarun baya ba.
APC: A haka Dino ya yi kokari a PDP
APC ta ce ba za a bugi yaro a hana shi kuka ba, amma dama ta san babu inda PDP za ta je a zaben bana, iyakarta Dino Melayen ya zo na uku.
Kakakin kwamitin kamfen Ododo ya kara da cewa kyau a binciki yadda Dino wanda bai kada kuri’arsa ba, ya iya samun kuri’u har 40, 000.
Sayen kuri'u a zaben Kogi, Imo da Bayelsa
Hukumar EFCC ta kama mutane 14 dauke da N11m da ake zargi za ayi amfani da su wajen sayen kuri’u a zaben jihohin Kogi, Imo da Bayelsa.
Rahoto ya zo cewa Mai magana da yawun bakin hukumar EFCC, Dele Oyewale ya ce sun karbe N9.3m a Bayelsa da kuma N1.7m a jihar Imo.
Asali: Legit.ng