Gwamnan Arewa Ya Sake Tsokano Fushin 'Yan PDP da Yi wa Tinubu Addu'a a Makkah

Gwamnan Arewa Ya Sake Tsokano Fushin 'Yan PDP da Yi wa Tinubu Addu'a a Makkah

  • Mai girma Bala Abdulqadir Mohammed ya na ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kama hanyar kawo cigaba a mulkin Najeriya
  • Sabanin jam’iyya da ke tsakanin Gwamnan na PDP bai hana shi yabon shugaban kasa ba, kuma ya yi masa addu’ar samun nasara
  • Gwamnan jihar Bauchi yana cewa yadda Tinubu ya kawo cigaba a Legas a shekarun baya, haka gwamnatinsa za ta gyara kasar nan

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed ya ce yayi imani cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai gyara kasar nan.

A ranar Laraba PM News ta rahoto Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed ya na yabon shugaban kasar wanda su ke jam’iyya dabam.

Kara karanta wannan

Abba v Gawuna: An Ja Hankalin Bola Tinubu Kan Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan Kano

Bola Tinubu tare da Gwamnoni
Bola Tinubu tare da Gwamnonin APC da PDP Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Gwamna Bala da Tinubu a Saudi

Gwamnan wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jihohin PDP ya yi wannan magana da yake magana da ‘yan jarida a kasar Saudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bala Abdulqadir Mohammed ya yi hira da manema labarai a garin Makkah a Saudi Arabiya.

NAN ta rahoto Gwamnan ya na cewa duk da sabanin siyasa da bambancin jam’iyya, ya na matukar girmama shugaban kasa Bola Tinubu.

Gwamnan PDP ya yabi mulkin APC?

"Dole mu yabawa kokarin Mai girma shugaban kasa da yunkurin farfado da tattalin arzikin da yake bukatar gyara.
Zuwa yanzu, mun ga matakai dabam-dabam da ya dauka da mu ke ganin zai kai mu zuwa ga sabuwar Najeriya.
Yayin da shugaban kasar ya yi wa Najeriya addu’a a wuri mafi tsarki a musulunci, ya ba ni kwarin gwiwar zai biya bukatar ‘Yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Wasu sun sace wayar tsohon minista a kotu wajen sauraron shari’ar zabe

Na yi masa addu’a domin idan ka yi wa shugabanni addu’a, a karshe ka yi wa kan ka ne."

- Gwamna Bala Mohammed

Kamar yadda aka ga cigaba a lokacin da Tinubu ya yi gwamna a Legas, jagoran na PDP ya ce haka shugaban kasar zai kawo cigaba a Najeriya.

Zuwa yanzu labarai sun zo cewa ziyarar Tinubu zuwa Saudiyya ta haifar da ‘da mai ido.

Gwamnonin PDP da 'Yan APC

Kwanaki aka ji mai taimakawa Atiku Abubakar a kan dabarun sada sadarwa ya caccaki wasu Gwamnonin PDP da su ka ziyarci Nyesom Wike.

Demola Rewaju ya aika martani ga wadanda aka gani sun je wajen Wike da yake aiki da gwamnatin APC, daga ciki har da shi Gwamnan jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng