Takaitaccen tarihin Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi mai jiran-gado

Takaitaccen tarihin Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi mai jiran-gado

A jiya ne hukumar zabe na INEC ta sanar da cewa Sanata Bala Mohammed ne ya lashe zaben gwamna da aka yi a jihar Bauchi inda ya doke gwamna mai-ci. Mun kawo kadan daga tarihin Kauran Bauchi.

1. Haihuwa da karatu

An haifi Bala Abdulkadir Mohammed ne a farkon Watan Oktoban 1958, kenan yana da shekaru 60 yanzu a Duniya. Bala Mohammed yayi karatu ne a gida har ya samu Digiri a harshen Turanci a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1982.

2. Aikace-aikace

Sanata Bala Mohammed ya soma aiki ne a matsayin mai kawowa gidan jaridar nan ta The Democrat rahoto a 1983 bayan ya kammala karatu. Daga nan kuma Mohammed ya koma aikin gwamnati har zuwa shekarar 2000.

3. Aikin Gwamnati

Bala Mohammed yayi aiki a ma’aikatu daban-daban wanda su ka hada da Ma’aikatar ma’adanai da ta harkokin cikin gida, da Ma’aikatar harkokin jirgin sama. A karshe dai yayi ritaya a matsayin Darekta a Nigerian Meteorological Agency.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya karyata cewa ya taya sabon Gwamna murna

Takaitaccen tarihin Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi mai jiran-gado
Bala Mohammed zai karbi mulkin Jihar Bauchi a Watan Mayu
Asali: Getty Images

Sabon gwamnan ya kuma yi aiki a hukumar da ke kula da jirgin kasa a Najeriya watau Nigerian Railway Corporation daga 2005 har 2007. Kafin nan kuma yayi aiki da Isa Yuguda a matsayin mai ba sa shawara daga 2000 zuwa 2005.

4. Siyasa

Bala Mohammed ya shiga siyasa ne bayan yayi ritaya inda yayi takara, ya kuma ci kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a 2007. Sanatan na ANPP ya samu matsala da tsohon Mai gidan sa watau Gwamna Isa Yuguda wanda ya koma PDP a mulkin 'Yaradua.

5. Minista

A 2010 ne shugaban kasa na rikon kwarya watau Goodluck Jonathan ya nada Bala Mohammed a matsayin Ministan babban birnin tarayya Abuja har zuwa 2015. Sanatan yana cikin wadanda su ka fara cewa a nada Jonathan kan mulki a wancan lokaci.

A zaben 2019 ne Bala Mohammed ya doke gwamna Mohammed Abubakar, na jam’iyyar APC inda ya samu kuri’u 515,113. APC ta samu kuri’a 500,625 ne a zaben inji hukumar INEC mai zaman kan-ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel