Gwamnan Arewa Ya Tsorata da Ganin Sabbin Fuskoki a Jihar Yayin da Ake Shirin Yanke Hukuncin Zabe
- Yayin da ake shirin yanke hukuncin shari'ar zaben gwamna a Nasarawa, Gwamna Sule ya fara korafi da zarge-zarge
- Gwamnan ya ce akwai wasu sabbin fuskoki da ke shigo wa jihar musamman a karamar hukumar Keffi da ke jihar
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnan jihar a gobe Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi korafi kan wasu sabbin fuskoki da ke shigo wa jihar a 'yan kwanakin nan.
Gwamnan ya yi wannan korafi ne yayin da ake shirin yanke hukuncin shari'ar zabensu a gobe Laraba 15 ga watan Nuwamba.
Mene Sule ke cewa kan hukuncin kotun?
Sule ya ce yawan shigowar mutane baki jihar musamman karamar hukumar Keffi ya fara ta da hankulan mutanen jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kirayi dukkan magoya bayansa da sauran jama'ar jihar da su yi kokarin danne zuciyarsu, Daily Trust ta tattaro.
Idan ba a mantaba, kotun zabe ta kwace kujerar Gwamna Sule na jam'iyyar APC kan wasu kura-kurai da aka samu a zaben gwamnan a jihar.
Wane hukunci karamar kotu ta yanke a baya?
Kotun ta tabbatar da David Ombugadu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, cewar Within Nigeria.
Daga bisani Gwamna Sule ya daukaka kara zuwa kotu don kalubalantar hukuncin karamar kotun da ta yi a Lafia babban birnin jihar.
Kotun daukaka kara ta sanya gobe Laraba 15 ga watan Nuwamba a matsayin ranar yanke hukuncin shari'ar zaben gwamnan jihar a Abuja.
Zaben Kogi: a karshe, Dino Melaye ya yi martani kan dokuwa da yake a zabe, ya fadi abin da INEC za ta yi
Kotu ta sanya ranar yanke hukuncin zaben Nasarawa
A wani labarin, kotun daukaka kara ta sanya ranar raba gardama a shari'ar da ake yi na zaben gwamnan jihar Nasarawa.
Kotun ta saka Laraba 15 ga watan Nuwamba a matsayin ranar yanke hukuncin shari'ar da ta bai wa Ombugadu na PDP nasara a zaben gwamnan.
Wannan na zuwa ne bayan kotun ta kwace kujerar Gwamna Sule Abdullahi na jam'iyyar APC a hukuncin karamar kotun.
Asali: Legit.ng