Kotu Ta Saka Ranar Yanke Hukunci Kan Shari’ar Zaben Gwamnan Jihar Arewa da Aka Kwace Kujerarshi

Kotu Ta Saka Ranar Yanke Hukunci Kan Shari’ar Zaben Gwamnan Jihar Arewa da Aka Kwace Kujerarshi

  • Kotun daukaka kara ta sanya ranar Laraba 15 ga watan Nuwamba a matsayin ranar yanke hukuncin zaben gwamnan jihar Nasarawa
  • Kotun ta bayyana haka ne ta bakin magatakardar kotun, Nasiru Alhassan a yau Litinin 13 ga watan Nuwamba a Abuja
  • Kotun kararrakin zabe a hukuncinta ta kwace kujerar Sule na APC tare da tabbatar da David na PDP a matsayin wanda ya lashe zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nasarawa - Kotun daukaka kara ta sanya ranar yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa.

Kotun ta sanya ranar Laraba 15 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a raba gardama a shari'ar da ake yi, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben kakakin Majalisa a APC , ta bayyana mai nasara

Kotu ta saka ranar yanke hukuncin zaben jihar Arewa a ranar Laraba
Kotu ta sanya ranar yanke hukuncin zaben gwamnan Nasarawa. Hoto: D. Ombugadu, S. Abdullahi.
Asali: Facebook

Wane hukunci karamar kotun ta yanke a Lafia?

Idan ba a mantaba, kotun kararrakin zabe ta kwace kujerar Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, kotun ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar PDP, David Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardar kotun, Nasiru Alhassan ya fitar a yau Litinin 13 ga watan Nuwamba a Lafia.

Tribune ta bayyana sanarwar kamar haka:

"Sauraran kararrakin zaben za a fara da misalin karfe tara na safe a kotun daukaka kara da ke Abuja."

Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamna Sule ya daukaka kara bayan rasa kujerarshi a kotun kararrakin zabe a Lafia.

Hausa Legit ta ji ta bakin wasu kan wannan sanarwar:

Kara karanta wannan

Zaben jihohi: Abubawa 3 da baku sani ba game da dan takarar jam'iyyar APC a zaben

Honarabul Chiroma ta ce:

"Ai babu maganar kotu a nan kawai APC ce za ta mallaki kujerar ganin yadda zabuka suka gudana a wannan satin."

Muhammad Adamu ya ce muna fatan kotun za ta yi adalci kamar yadda ta yi a wasu jihohin Arewa kamar Kano.

Salisu Adamu ya ce:

"Wannan nasarar PDP ce saboda dukkan alamu sun nuna David ne zai yi nasara a wannan shari'a."

Kotun ta kwace kujerar Gwamna Sule

Kun ji cewa, Kotun kararrakin zabe ta kwace kujerar Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.

Har ila yau, kotun ta tabbatar da nasarar David Ombugadu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.