Labari Da Dumi-Dumi: Hukumar INEC Ta Sanar da Duka Wuraren da Aka Soke Zabe a Kogi

Labari Da Dumi-Dumi: Hukumar INEC Ta Sanar da Duka Wuraren da Aka Soke Zabe a Kogi

  • INEC ta tabbatar da cewa an dakatar da shirya zabe a wuraren da aka samu sakamakon bogi suna yawo a kogi
  • Kwamishinan Hukumar zaben ya fitar da jawabi cewa ba za a karbi duk wani sakamako da ba daga rumfa ya fito ba
  • Muhammad Kudu Haruna ya shaida cewa zuwa yammacin Lahadi za a ji matsayar da INEC ta dauka a zaben jihar

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kogi - Hukumar INEC ta bada sanarwar dakatar da zaben sabon gwamna a wasu daga cikin bangarorin jihar Kogi.

Hukumar gudanar da zabe mai zaman kan ta watau INEC ta fitar da sanarwa a shafin Twitter a yammacin yau Asabar.

Kogi.
Wasikar INEC a kan zaben Kogi Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Sanarwar ta fito ne daga ofishin Kwamishinan yankin Arewa maso tsakiya wanda ya na cikin kwamitin watsa labarai.

Kara karanta wannan

Dino Melaye ya kauracewa zaben gwamnan Kogi? Gaskiya ta bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammad Kudu Haruna ya ce hukumar zabe ba za ta karbi sakamakon wuraren da aka samu kuri’un bogi a Kogi ba.

Zaben Kogi: Jawabin Kwamishinan INEC

"Hukumar ta samu rahoton da ya shafi samun malaman zabenmu a jihar Kogi da saba doka, musamman lamarin sakamakon kuri’u kafin a fara dangwala kuri’u.
Rahotanni sun nuna lamarin ya auku ne a kananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi da Okene.
Idan abin ya fi kamari a Ogori/Magongo ya shafi rumfunan zabe tara a cikin goma.
Ko kadan ba za a yarda da wannan ba. Duk sakamakon da bai fito daga hannun hukuma a rumfunan zabe ba, ba zai samu karbuwa ba."

- Muhammad Kudu Haruna

Sanarwar ta ce a sakamakon haka an dakatar da zaben Gwamnan a mazabu tara da ke karamar hukumar Ogori/Magongo da ke Kogi.

Kara karanta wannan

Zaben jihohi: Abubawa 3 da baku sani ba game da dan takarar jam'iyyar APC a zaben

Mazabun nan sun hada da Eni, Okibo, Okesi, Ileteju, Aiyeromi. Ragowar kuma su ne Ugugu, Obinoyin, sai kuma Obatgben da Oturu.

Muhammad Haruna ya shaida cewa ana binciken abin da ya faru a sauran kananan hukumomi, kuma za a fitar da matsaya nan da sa’o’i 24.

INEC ta sanar da cewa ba za ta bari ayi magudi a zaben da ake gudanarwa a jihar ba. Dama can Dino Melaye ya yi irin wannan kira.

EFCC da DSS wajen zaben Kogi

Dazu an ji labari DSS suna ta sintiri a rumfar zaben da ake tsammanin ‘Dan takaran PDP a zaben watau Dino Melaye zai jefa kuri’arsa.

Haka zalika hukumar EFCC ta aika runduna ta musamman watakila saboda masu sayen kuri’u domin ganin abubuwa sun tafi daidai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel