Zaben 11 Ga Nuwamba: Jerin Gwamnonin Jihar Kogi Daga 1999 Zuwa Yanzu
Jihar Kogi, Lokoja: Sabon gwamna zai maye gurbin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, bayan mutanen jihar Kogi sun kada kuri'unsu a jihar a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Ana ta yin lissafe-lissafe, gabanin zaben gwamna na jihar Kogi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma gwamnan mai ci a yanzu ya fito ne daga yankin Kogi ta Tsakiya, yayin da mataimakinsa shi kuma daga gabashin jihar ya fito.
Tun shekarar 1999, gwamnoni uku, marigayi Abubakar Audu, Alhaji Ibrahim Idris da Kyaftin Idris Wada sun fito ne daga Kogi ta Gabas, Alhaji Yahaya Bello, (Kogi ta Tsakiya) yayin da Cif Clarence Olafemi (Kogi ta Yamma) ya mulki jihar na rikon kwarya na kwana 60.
Wa'adin tsaffin gwamonin ya nuna cewa Kogi ta Gabas ta mulki jihar na shekaru 16, daga 1999 zuwa 2016, yayin da Kogi ta Tsakiya, inda gwamna mai ci yanzu ya fito, Bello, ce ke mulkar jihar tun 2016 zuwa yanzu.
Sai dai, mutane jihar za su zabi wanda zai jagorance su daga cikin manyan yan takarar a zaben, cikinsu har da dan takarar da Bello ya ke goyon baya, Usman Ododo.
A yayin da ake cigaba da hasashe kan wanda zai gaji Bello, cikin yan awanni daga yanzu daga masu sharhi kan siyasa da fastoci da jam'iyyun siyasa, Legit Hausa ta yi waiwaye don kawo muku jerin gwamnonin da suka mulki jihar.
Cikakken jerin tsaffin gwamnonin da suka mulki jihar Kogi zuwa yanzu
Augustine Aniebo (1998 - 1999)
Augustine Aniebo, wanda aka haifa a ranar 23 ga watan Maris na 1950, birgediya janar na soji wanda ya mulki jihar a matsayin gwamnan soji daga 1998 zuwa 1999.
Yayin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar, ya mika mulki ga gwamnan farar hula Abubakar Audu a ranar 29 ga watan Mayun 1999, a farkon jamhuriya ta hudu.
Aniebo ya bar ofis a ranar 29 ga watan Mayun 1999 ba tare da rantsar da magajinsa ba, ya mika mulki ta hannun wakili.
Abubakar Audu (1999 - 2003) Jam'iyyar All Peoples Party, (APP)
Yarima Abubakar Audu shine gwamnan farar hula na biyu da aka zaba matsayin gwamnan jihar Kogi.
An haife shi ne a ranar 24 ga watan Oktoban 1947, amma ya rasu a ranar 22 ga watan Nuwamban 2015.
Marigayi Audu ma'aikacin banki ne kuma dan siyasa kuma shine gwamnan farar hula na farko a jihar Kogi.
Ya mulki jihar sau biyu (na farko a Jamhuriya ta uku sannan na biyu a Jamhuriya ta Hudu). Wa'adinsa na farko ya fara daga Janairun 1992 zuwa Nuwamban 1993 na biyun kuma daga 29 ga watan Mayun 1999 zuwa 29 ga watan Mayun 2003.
Ya rasu sakamakon gyambon ciki kafin sanar da sakamakon zabe a ranar 22 ga watan Nuwamban 2015, yayin neman tazarce a matsayin gwamna a karkashin jam'iyyar APC mai mulki.
Ibrahim Idris (2003 - 2008, 2011) (PDP)
Idris, dan kabilar Igala, ya zama gwamnan farar hula na biyu a jihar Kogi karkashin PDP a Afrilun 2003, bayan yin galaba kan Audu Abubakar na APP.
Dan siyasan kuma dan kasuwa ya mulki jihar daga 2003 zuwa 2011, sannan surukinsa Kayfin Idris Wada, wanda ya ci zaben Disamban 2011 ya gaje shi, ya yi rantsuwar kama aiki a Janairun 2012.
Clarence Olafemi (2008 - 2011) (PDP)
Olafemi ya mulki mutanen Kogi a 2008 a matsayin gwamnan rikon kwarya, (daga 6 ga watan Fabrairun 2008 zuwa 29 ga watan Maris din 2008).
Ya kama aiki bayan cire gwamna, Ibrahim Idris da mataimakinsa Philip Salawu da Kotun Koli ta yi.
Olafemi, tsohon kakakin majalisar jihar Kogi, ya mika mulki ga Ibrahim Idris a ranar 29, 2008, bayan Idris ya lashe sabon zabe.
Idris Wada (2011 - 2016) (PDP)
An haifi Idris Ichala Wada a ranar 26 ga watan Agustan 1950, kuma tsohon matukin jirgin sama ne gami da dan siyasa.
Ya kafa tarihi a matsayin gwamnan farar hula na uku a jihar Kogi karkashin jam'iyyar PDP.
Yahaya Bello ya gaje shi a ranar 27 ga watan Janairun 2016, bayan ya sha kaye a zaben gwamnan jihar Kogi a 2015.
Yahaya Adoza Bello (APC)
Bello shine gwamnan jihar Kogi mai ci a yanzu kuma gwamnan farar hula na hudu a jihar.
An haifi Bello ne a ranar 18 ga watan Yunin 1975, dan kasuwa ne kuma dan siyasa wanda ya mulki jihar tun 2016.
Bello shine gwamna mafi karancin shekaru a Najeriya tsawon shekarun da ya yi a ofis, karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Bello zai mika mulki ga magajinsa bayan sakamakon zaben ranar Asabar 11 ga watan Nuwamban 2023.
Kogi 2023: Fitaccen malami ya yi hasashen wanda zai lashe zaben gwamna
A wani rahoton shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC mai mulki a kasa ne za ta lashe zaben gwamna na jihar Kogi da za a gudanar ranar Asabar 11 ga watan Nuwamban 2023.
Usman Ahmed Ododo, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC shine wanda Gwamna Yahaya Bello mai ci yanzu ya ke goyon baya.
Asali: Legit.ng