Bola Tinubu Ya Tuno MKO Abiola, Ya Ba ‘Diyarsa Mukami a Fadar Shugaban Kasa

Bola Tinubu Ya Tuno MKO Abiola, Ya Ba ‘Diyarsa Mukami a Fadar Shugaban Kasa

  • Da alama Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada mai ba shi shawara a bangaren shugabanci da harkokin ‘yan kasa
  • Bayanai sun nuna Rinsola Abiola ta samu shiga cikin hadiman shugaban kasa, sanarwa ba ta fito ba tukuna har yau
  • Mahaifin ya na cikin wadanda su ka jawo hannun Bola Tinubu, su ka nuna masa yadda ake siyasa a shekarun 1990s

Abuja - Ana yawo da labari cewa Bola Ahmed Tinubu ya shiga gidan Marigayi Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ya bada mukami.

A yammacin Alhamis dinnan labarai su ka fara yawo cewa Rinsola Abiola ta zama babban mai taimakawa shgaban kasa a harkar shugabanci.

Rinsola Abiola
Bola Tinubu ya ba Rinsola Abiola mukami Hoto: @ShinaShine
Asali: Twitter

Baya ga sha’anin shugabanci, Legit ta fahimci aikin ya hada da harkar kula da ‘yan kasa.

Wa ya sanar da nadin Rinsola Abiola?

Rinsola Abiola ta tabbatar da haka da ta rika sake wallafa labaran da su ke fitowa daga wajen masoya da abokan arzikinta a dandalin X.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa Sun Tsoma Baki a Rigingimun Dauda/Matawalle da BUA/Dangote

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zuwa yanzu babu wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, amma ‘yar siyasar ta tabbatar da labarin, jama’a kuma suna ta yi mata murna.

Sai dai ta fitar da jawabi na musamman a jiya, ta godewa Mai girma shugaban kasa da ya ba ta wannan matsayi ta yi aiki a gwamnatinsa.

Mutanen Ogun sun taya Abiola murna

Shugaban karamar hukumar Abeokuta ta Arewa, Prince Adebayo Abdussalam Ayorinde ya fitar da jawabi, ya na mai yi wa Abiola barka.

Mai girma Prince Adebayo Abdussalam Ayorinde ya ce a madadin mutanen Abeokuta, suna fatan mukamin ya kawo mata karin nasara.

Sanarwar ta ce ‘yar siyasar za ta yi aiki hannu da hannu da ma’aikatar matasan Najeriya.

Rinsola Abiola a jam'iyyar APC

Ga wadanda ba su da labari, Rinsola cikakkiyar ‘yar APC ce wadanda aka kafa jam’iyyar da su, su ne bangaren shugabannin mata a tafiyar.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Tinubu ya amince da sabbin nade-nade 20, jerin sunaye

A shekarar 2015, ta na cikin matasan da su ka shiga majalisar amintattu (BOT) na APC, ta yi karatu da ayyuka iri-iri a Najeriya da kasar waje.

Daga baya Ms. Abiola ta sauya sheka bayan aiki da Rt. Hon. Yakubu Dogara a lokacin ya na rike da shugabancin majalisar wakilan tarayyar kasa.

Sabuwar hadimar shugaban Najeriyan ta taba ficewa daga APC, amma daga baya ta dawo, kuma ta ba Tinubu/Shetimma gudumuwa a 2023.

Me 'Yan APC su ke fada a kan Rinsola Abiola?

Legit ta yi magana da Sahabi Sufyan wanda ya shaida mana an dauko wanda ta cancanta, ya na cikin wadanda su ka nemi kujerar shugaban matasa a APC.

"Na san ta na tsawon lokaci, ta sha bam-bam da sauran matasa. Jagorar matasa ce mai kazar-kazar wanda ta bada gudumuwa a takarar shugaban kasa
Ta kafa kungiyar mata da ta kira "Progressives Sisters Network". Ina sa ran za ta sauke nauyi, ba ni da tababa a kan ta, ina sa ran za ta yi aiki da kyau."

Kara karanta wannan

A shirya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi mamayar da Tinubu zai yi wa 'yan boye dala

- Sahabi Sufyan

Bola Tinubu da 'yan gidan Abiola

A watann Satumba labari cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba wani yaron marigayi Mashood Abiola kujerar hadimin a fadar shugaban kasa.

Jamiu Abiola ya zama mai bada shawara a kan bangaren ayyuka na musamman. Sanarwar da aka fitarta ce Abiola ya yi karatu a New York.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel