Sunaye: APC ta samu sabbin mambobin BoT a karkashin Mai Mala Buni

Sunaye: APC ta samu sabbin mambobin BoT a karkashin Mai Mala Buni

Kwamitin shugabancin rikon kwarya na jam'iyyar APC a karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya fara samun nasara a kokarinsa na yin sulhu a cikin jam'iyyar APC.

A ranar Litinin ne wasu shahada'un 'ya'yan jam'iyyar APC daga cikin mambobin kwamitin koli na jam'iyyar suka gudanar da wani muhimmin taro tare da kafa wata sabuwar kungiya ta ma su dattako.

Kungiyar ta nada shugabanninta tare da aika takardar sanarwa ga shugaban riko na jam'iyyar APC, gwamna Mai Mala Buni.

A cikin takardar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar; Honarabul Abubakar Saadu, da sakatarensa; David Okumba, kungiyar dattijan ta bawa Buni tabbacin samun goyon bayan mambobinta a kokarinsa na mayar da jam'iyyar APC kan hanyar zaman lafiya.

Kazalika, kungiyar ta yabawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bisa shawarar da ya yanke na rushe kwamitin gudanarwa na APC (NWC) wanda tsohon shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomhole, ya kafa.

Zababbun mambobin kungiyar sun hada da; Honarabul Abubakar Sadiq Saadu – daga arewa maso yamma a matsayin shugaba, Dakta Racheal Akpabio – daga yankin kudu maso kudu a matsayin mataimakin shugaba, David Okumgba – daga yankin kudu maso kudu a matsayin sakatare, Abubakar A. Musa – daga yanlin arewa maso gabas a mataimakin sakatare.

Sunaye: APC ta samu sabbin mambobin BoT a karkashin Mai Mala Buni
Mai Mala Buni
Asali: Original

Sai Lawal Kolade – daga yankin kudu maso kudu a matsayin ma'aji, Terver Aginde – daga yankin arewa ta tsakiya a matsayin sakataren tsare - tsare, Honarabul Muhammed S. Ibrahim daga yankin arewa maso yamma a matsayin sakataren yada labarai da Barista Tanko Zakari – daga yankin arewa ta tsakiya a matsayin mai bayar da shawara a kan harkokin shari'a.

DUBA WANNAN: Badakala: An bankado wata makarantar FG da ake biyan mai shara albashin N32m

Sauran sun hada da; Muhammad Azare, Nduka Anyanwu, Bolaji Repete Hafeez, Hon. Ihuoma Onyebuchukwu, Abubakar Ajiya, Abdulmunaf Muh’d, John Uwaedu, Adie Ferdinand Atsu da Jock Alamba.

Dangane da sabbin mambobin kwamitin amintattun na APC (BoT), jam'iyyar ta amince da nada Alhaji Nasiru Danu daga yankin arewa maso gabas a matsayin shugaba, Sunday Jacob daga yankin kudu maso gabas a matsayin sakatare.

Sauran sun hada da Cif Koteteh Ibadan daga yankin kudu maso yamma a matsayin mamba, Alhaji Zakari Muhammad daga yankin arewa ta tsakiya a matsayin mamba da Alhaji Shuaibu Abdulrahman daga yankin arewa maso gabas a matsayin mamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng