Hawan jini Ya 'Kashe' Mutane da Kotu ta Tsige ‘Dan Majalisar da ya Ci Kuri’u 95, 000

Hawan jini Ya 'Kashe' Mutane da Kotu ta Tsige ‘Dan Majalisar da ya Ci Kuri’u 95, 000

  • Hon. Dachung Musa Bagos ya rasa kujerar da yake kai a majalisar wakilan tarayya a sakamakon hukuncin kotun daukaka kara
  • ‘Dan majalisar na mazabar Kudanci da Gabashin Jos ya ce akwai rashin adalci a yadda aka raba ‘yan jam’iyyar PDP da mukamansu
  • Har yanzu Dachung Musa Bagos ya hakikance cewa bai dace kotu ta tsige shi da wasu Sanatoci kan abin da ya faru kafin zabe ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Dachung Musa Bagos ya yi Allah-wadai da hukuncin da kotu ta zartar a shari’ar zabensa, inda aka tsige shi daga majalisar tarayya.

A wata hira da aka yi da Hon. Dachung Musa Bagos a shirin siyasa na tashar Channels, ya kamanta abin da ya faru da juyin mulkin sojoji.

Kara karanta wannan

Wayyo Gida Na: Jigon PDP Ya Kai Kuka, Gwamnatin APC Za Ta Rusa Masa Muhalli

Majalisar wakilai
PDP ta rasa mutane a Majalisar wakilai Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

Duk da shi ba jami’in soja ba ne, tsohon ‘dan majalisar tarayyan ya ce abin da ya faru da 'yan PDP a kotun daukaka kara kamar shari’an sojoji ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba ayi wa 'Yan Majalisan PDP adalci ba?

Dachung Musa Bagos ya na ganin babu adalci a hukuncin da aka yi, inda kotu ta sauke ‘yan majalisa da Sanatoci bakwai daga jihar Filato.

Abin da ya kara fusata tsohon ‘dan majalisar shi ne duka wadanda aka sauke ‘yan PDP ne, an fara haka ne tun daga kan kotun korafin zabe.

Dachung Bagos wanda ya wakilci Jos ta Kudu/Jos ta Gabas ya ce cikin wadanda kotu ta sauke, babu wanda bai ci zabensa da rata mai yawa ba.

A na sa zaben na Gabashi da Kudancin Jos, Bagos ya fadawa tashar cewa ya ba wanda ya zo na biyu a LP ratar kuri’u sama da 60, 000.

Kara karanta wannan

Dawowar Harin Boko Haram a Wasu Jihohi Ya Fara Tada Hankalin ‘Yan Majalisan Tarayya

Mutane sun mutu saboda tsige 'Yan PDP a kotu

Mutanen da ake wakilta sun san an yi masu rashin adalci; a tsige ‘yan majalisa biyar da Sanatoci biyu, abin ban mamaki ne.
Zan iya fada maka cewa a halin yanzu, mun rasa mutane hudu, mutane sun mutu a jihar Filato saboda abin da ya faru.
Akwai matar da ke rike da jariri, da labari ya zo mata sai ta fadi, aka garzaya da ita asibiti, a nan ta yi sallama da duniya.

Ministan Tinubu ya doke PDP a kotu

Ana da labari Simon Lalong ya yi nasara a kotun daukaka kara, inda aka tabbatar da hukuncin kotun zabe a shari'ar Sanatan Filato ta Kudu.

Bagos ya ce labarin ba PDP kadai ya girgiza ba, mutanen mazabarsa sun kamu da hawan jini domin ba ayi wa talaka da ya yi zabe adalci ba.

'Dan siyasar ya ce AVM Napoleon Binkap Bali mai ritaya ya yi galaba kan Simon Lalong da aka yi zaben da makamanciyar ratarsa mai yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng