Da kyau: Kakakin majalisar wakilai, Gbajabiamila, ya nada diyar Ganduje matsayin babbar hadimarsa

Da kyau: Kakakin majalisar wakilai, Gbajabiamila, ya nada diyar Ganduje matsayin babbar hadimarsa

Kakakin majalisar dattawa, Femi Gbajabiamila, ya nada diyar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kuma surukar tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, Fatima Ganduje-Ajimobi, a matsayin hadimarsa kan kungiyoyin fafutuka.

Mijin Fatima, Idris Ajimobi, dan tsohon gwamnan jihar Oyo, ya alanta wannan abu ne a shafin ra'ayi da sada zumuntarsa ta Instagram.

Yace: "Fatima Abiola-Ajimobi, ban sani ko har yanzu kin dauke maganata da gaske ba saboda kullum ina maimaitawa; ke fitacciyar mace ce."

"Na shaida lokutan da ki ka jajirce kan wasu kalubale da ki ka fuskanta a rayuwa amma baki gaza ba. Addu'ata gareki uwargidata shine Allah ya kare miki karfin hali."

"A kananan shekarunki, ina mai farin cikin taya ki murnar nadaki babbar hadimar kakakin majalisar wakilan tarayya kan kungiyoyin sa kai da fafutuka."

A bangare guda, Bayan kwanaki 100 na farko a bisa kujerar mulki, wata cibiyar dimokuradiyya ta Afirka mai tushe a birnin Dakar na kasar Senegal, ta zabi gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin gwamnan da ya fi kowanne kwazo a halin yanzu a Najeriya.

Cibiyar mai akidar dimokuradiyya ta ADAN, African Democracy Assessment Network, ta ayyana gwamna Ganduje a matsayin gwamnan da ya yi wa sauran gwamnonin Najeriya fintinkau ta fuskar kwazo a bisa kujerar mulki, lamarin da ta ce ya cancanci kyauta ta musamman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel