Abba v Gawuna: Abubuwa 13 da Kotun Daukaka Kara Za Ta Duba a Shari'ar Zaben Gwamnan Kano

Abba v Gawuna: Abubuwa 13 da Kotun Daukaka Kara Za Ta Duba a Shari'ar Zaben Gwamnan Kano

  • Kotun daukaka kara ta fara sauraron shari’ar da Abba Kabir Yusuf ya gabatar a kan zaben Gwamnan jihar Kano na 2023
  • Gwamnan ya na mai kalubalantar hukuncin da kotun sauraron korafin zabe wanda ya tsige shi daga kan kujerar da yake kai
  • Lauyan da ya tsayawa Abba Yusuf, Wole Olanipekun ya gabatar da jerin korafi sama da 40 da yake so babban kotun ta duba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Legit ta jero muhimmai daga cikin korafin da Wole Olanipekun SAN ya mikawa kotu a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf a Abuja.

1. APC ta makara wajen gabatar da hujjoji a zaben Kano

An gabatar da hujjoji a ranar 22 ga watan Yuli 2023 bayan an rufe kofar yin hakan a ranar 15 ga watan Yuli 2023 har an fara kira shaidar wanda ake kara.

Kara karanta wannan

An Sabunta: Cikakken jerin gwamnonin da kotu ta kwace kujerunsu kawo yanzu

Gwamnan Kano
Shari'ar zaben Gwamnan Kano Hoto: Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Hukuncin zaben takarar Abba v Gawuna ta Zoom

Wole Olanipekun ya yi ikirarin cewa ya kamata kotu ta zauna ne kamar yadda ta rika sauraron korafin a baya, amma a karshe sai aka yi shari’a ta kafar Zoom.

3. "Nasiru Gawuna bai cika sharudan cin zabe ba"

Lauyoyin APC ba su fadawa kotu yadda Nasiru Yusufu Gawuna ya samu 25% a biyu bisa ukun kananan hukumomin Kano, wanda wajibi ne a sashe na 179(2).

4. Kotun zaben Kano ba ta san Gawuna ba

Lauyan wanda ya daukaka kara ya zargin kotun baya da biyawa APC bukatar da ba ta nema ba kuma ya ce ba a hada da Nasiru Gawuna a karar zaben ba.

5. Zaben Kano: Cancantar mai bada shaida

A cewar lauyan da ya tsayawa Gwamna, babu takardar karatu da aka gabatar mai nuna wanda ya bada shaida masani ne, akasin abin da dokar shaida ta bukata.

Kara karanta wannan

Shari’ar Zabe: Gwamnatin Abba Gida-Gida ta yi muhimmin kira kafin a shiga Kotu

6. APC v NNPP: Karbar shaida da Hausa a Kotu

Masu korafi sun ce lauyoyin APC sun kawo marasa jin Turanci domin bada shaida duk da Ingilishi ne yaren kotu, su ka bukaci a rusa shaidar wadannan mutane.

7. Hujjar zaman Abba ‘Dan NNPP

Duk da an rufe maganar zama ‘dan jam’iyya, lauyoyi sun ce rajista kadai ba za ta nuna wanene ‘dan jam’iyya ba kamar yadda kotu ta yi hukunci a babban zaben 2003.

8. Ratar Gawuna da Abba a 2023

Karar Wole Olanipekun ta kara da cewa kotun korafin zabe ba ta bi ka’idar da aka yanke a game da ratar lashe zabe ba, inda aka ce APC ta bada tazarar kuri’u 36, 719.

9. Kuskuren aiki da dokar zabe

Fitaccen lauyan ya yi ikirarin Alkalan da su ka fara sauraron shari’ar zaben Kano ba su yi amfani da dokar kasa da dokar bada shaida wajen karbar shaidun APC ba.

10. Soke kuri’un Abba Kabir Yusuf

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun haramta murna ana shirin yanke hukunci a shari’ar zaben gwamna

NNPP ta zargi Kotu da cewa ita ta ba kan ta aikin sokewa Abba Kabir Yusuf kuri’u duk da babu dalilin yin haka a doka, kuma ba a bukaci NEC ta kare kan ta ba.

11. An cirewa Abba/NNPP halatattun kuri’u

Idan aka duba sashe na 63 na dokar zabe, Olanipekun ya ce babu inda aka wajabta rubutu sunan malamin zabe, hatimi da kwanan wata, don haka an cire kuri’un halal.

12. Daga ina APC ta fito da kuri’u 165, 000 a Kano?

A madadin Gwamna Abba, lauyoyi sun ce ba a kira wakilan jam’iyya su bada shaida daga rumfuna ba, kuma doka ba ta bada damar bambanta kuri’un NNPP da APC ba.

Akwai alamun nasara - Lauyan NNPP

Barista Bashir Lawal Tudun Wazirci ya shaidawa Legit cewa nasarar kujerun majalisa manuniya ce da ke nuna idan Allah ya yarda za su yi nasara.

“Wadannan nasarori da mu ke samu ya nuna muna kan galaba. Kuma ya nuna abin da mu ke fada na cewa karamar kotu ba ta fahimci dokokin zaben nan, ta yi masu adalci ba.

Kara karanta wannan

'Inconclusive': Kotu ta ayyana zaben gwamnan Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba, za a sake zabe

Kuma idan ka duba mun samu hukunce-hukunce kusan 11 kenan na majalisar tarayya, wanda daga ciki kusan uku an karbe mana kujeru ne, kuma yanzu duk sun dawo.
Wannan manuniya ce da ke nuna idan Allah ya yarda, shi ma na Gwamna din da mu ka gabatar, da yarda Allah za mu samu nasara.”

- Bashir Lawal Tudun Wazirci

Ana da labari Lauyoyi irinsu Femi Falana SAN da Barista Kabir Akingbolu sun soki hukuncin Alkalai a shari’ar Gwamnan Kano, su ka ce ba ayi adalci ba.

Kabir Akingbolu Esq ya shaida cewa hukuncin shari’ar zaben Shugaban kasa (PDP da LP vs APC) ya nuna kuskuren da aka tafka a zaben jihar Kano na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng